✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma —Sheikh Rijiyar Lemo

Shugabanci na kwarai har koyaushe yana aikata abin da zai saukake wa al’umma rayuwarsu ne.

Bajimin Malamin addinin Islama, Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, ya yi kira ga Musulmi da kuma mahukunta a Najeriya dangane da tababar da ta dabaibaye batun sauya fasalin takardun kudin kasar.

Cikin wani sako da Sheikh Rijiyar Lemo ya wallafa ranar Asabar a shafinsa na Facebook, ya ja hankalin Musulmi da duk sauran masu ruwa da tsaki kan abin da ya kamaci kowanne bangare dangane da batun sauya fasalin kudin kasar.

Ga kiraye-kiraye, tunatarwa gami da jan hankali da shehin malamin ya yi:

1. Allah (SWT) yakan zo da abubuwa masu dadi da marasa dadi a rayuwa, don su zamanto jarraba wa ga bayinsa, domin ya bayyana wadanda suka fi kyautata ayyukansu. Wajibi ne ga duk wani Musulmi ya rika halarto da wannan ma’ana a zuciyarsa duk sanda ya ga an shiga wani yanayi bako a rayuwa. Ya yi kuma kokarin cinye wannan jarrabawa.

2. Hukumar Samar da Takardun Kudade karkashin Babban Bankin Kasa (CBN), tare da sahalewar Shugaban Kasa sun yi tunanin sake fasalin wasu takardun kudaden Najeriya domin wasu maslahohi da suka hango da kuma magance wasu matsaloli. Muna musu kyakkyawan zato cikin wannan kuduri nasu, muna kuma fatan a yi nasara cikin hakan.

3. Amma duk da haka, wajen tabbatar da waccan kyakkyawar manufa, talakawa a Najeriya, sun shiga wani mawuyacin hali kuma mai ban tausayi, musamman a kauyukanmu na Arewa. Don haka muna rokon hukumar da wannan abu ya shafa da su duba halin da jama’a suke ciki, su amsa kiraye-kirayen al’umma na kara wa’adin da suka saka na dakatar karbar tsofaffin kudi, ko kuma su yi wa tsarin gyaran fuska, don fitar da al’umma daga wannan kangi mawuyaci.

4. Shugabanci na kwarai har koyaushe yana aikata abin da zai saukake wa al’umma rayuwarsu ne ta yau da kullum, da kuma sa ma musu walwala a harkokinsu, da guje wa jefa su cikin tsanani da wahalhalu.

5. Fatanmu hukuma za ta dubi wannan lamari ta kuma yi abin da ya dace. Allah ya musu kyakkyawan jagoranci, ya ba mu zamanan lafiya da arziki mai dorewa a kasarmu. Amin.