Cardi B ta shirya bikin daurin aure bayan shekara 5 a gidan miji | Aminiya

Cardi B ta shirya bikin daurin aure bayan shekara 5 a gidan miji

Cardi B, da mijinta Offset
Cardi B, da mijinta Offset
    Rahima Shehu Dokaji

Fitacciyar mawakiyar duniya Cardi B, ta ce kwanan nan za a gudanar da bikin daurin aurenta da mijinta Offset da aka yi a sirrance shekaru biyar da suka gabata.

Mawakiyar wadda sunanta na asali Belcalis Alcantara, ta wallafa a shafinta na Twitter cewa lokaci ya yi da ya kamata a yi bikin.

“Shekaru biyar ke nan da aurena, don haka lokaci ya yi da zan shirya bikin da ban yi ba a baya,” ta wallafa.

Cardi B ta kuma wallafa hoton bikin zagayowar ranar aurensu da sahibin nata, tana sanye da riga da wando, rike da hannun mijinsa.

A shekarar 2020 ne dai suka rabu da mijin nata, bayan ta zarge shi da lalata da wata, sai dai daga baya sun daidaita sun maida auren nasu.

Kwanaki kadan da suka gabata ne kotu ta yanke mata hukuncin hidimta wa al’umma na wani lokaci, bisa samun ta da laifin yi wa wasu mata da take zargi da yin lalata da mijinta dukan tsiya.

Cardi B da Offset dai na da ’ya’ya biyu tare, masu suna Kulture da Wave.