✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Carlos Tevez ya ajiye kwallo

Na rasa babban masoyina lamba daya.

Tsohon dan wasan tawagar Argentina da Manchester United da Manchester City da West Ham, Carlos Tevez ya sanar da yin ritaya daga taka leda.

Carlos Tevez wanda ya sanar da kawo karshen kwallon kafa, ya ce mutuwar “masoyinsa lamba daya” wato mahaifinsa, Segundo Raimundo, shi ne babban dalilin da ya sa ya yanke shawarar daina taka leda.

Dan kwallon ya sanar cewar ya yi dukkan abin da zai yi a kwallon kafa, amma yanzu mutuwar mahaifinsa a watan Fabrairun bara, ta sanya shi ajiye takalma, duk da wasu kungiyoyi sun gabatar masa da tayin bukata a kansa.

Rabon da Tevez mai shekara 38 ya taka leda tun bayan Yunin 2021, bayan da ya bar kungiyarsa da ya fara wasa tun yana matashi Boca Juniors.

Tsohon dan wasan Manchester United da City a yanzu yana shirin zama daraktan kula da tsare-tsare kuma zai yi aiki kafada da kafada da Carlos Chapa Retegui, wanda tsohon dan wasa ne kuma kocin kungiyar kwallon hockey ta Argentina.

Tevez ya taka leda a Juventus da kungiyar Brazil, Corinthians da zuwa Boca Juniors karo uku da Shanghai Shenhua ta China.

Tevez ya lashe kofuna da dama a tsawon shekaru 20 da ya yi yana taka leda, ciki har da kofunan manyan gasannin Argentina guda biyar a tsawon zama karo uku da ya yi tare da Boca Juniors.

A lokacin da yake taka leda a Ingila, Tevez ya lashe Kofin Zakarun Turai tare da Manchester United a shekarar 2008, da kuma kofunan gasar Firimiya guda biyu tare da Reds din kafin ya tafi da abokiyar hamayyarta wato Manchester City.

Dan kasar Argentina ya sake lashe gasar Firimiyar Ingila karo na uku a City, inda ya lashe kofin FA a kakar 2010-11 karkashin jagorancin Roberto Mancini.

Tevez ya kuma lashe kofuna hudu a lokacin da yake tare da Juventus na Italiya, ciki har da kofunan Seria A guda biyu, yayin da ya lashe gasar cin kofin FA na kasar Sin a cikin kankanin lokacin da ya yi a Shanghai Shenhua.

A matakin kasa, a shekarar 2004 Tevez ya lashe lambar zinare a gasar Olympics da aka buga wa kasarsa ta Argentina a Athens.

A gasar ce kuma Teves ya lashe kyautar dan wasa mafi zira kwallaye bayan ya jefa guda takwas a koma. Ya buga wa Argentina wasanni 75 a tarihi.