✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN ya boye sabbin takardun Naira —Gwamnan Jigawa

Gwamna Badaru ya yi zargin Babban Bankin ya kwashe sabbin Naira ya boye

Gwamnan Jigawa, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya zargi Babban Bankin Najeriya da boye sabbin takardun Naira lamarin da ya ce ya sa al’ummar jihar ke kwana bin layin domin cirar kudi a ATM.

Badaru ya fadi hakan ne ta bakin Kwamishin Kudi da Bunkasa Tattalin Arzikin Jihjar, Babangida Umar Gantsa a ranar Laraba.

“Gwamnan Badaru ya yi matukar damuwa da yadda jama’a ke fama da wahalar da CBN ya kirkiro na sake fasalin Naira wanda hakan ya sa ake fama da karancin kudi a bankuna,” in ji Kwamishinan.

Gwamnan ya yi zargin CBN ya kwahsi sabbin takardun na Naira ya boye wanda hakan ya jefa talakawansa cikin tasku.

Ya ce ’yan jihar na fama saboda harkokin kasuwanci da sauransu sun tsaya sakamakon rashin sabbin takardun Naira.

Lamarin da a cewarsa ya kai ga mutane na kwana a gindin ATM suna bin layi don neman cire kudi.

Daga binciken da ya yi a bankuna, Gwamnan ya ce ya gano CBN ba ya bai wa bankunan jihar wadatattun sabbin takardun Naira da ya kamata su loda a ATM don amfanin jama’a.

“Jami’an da aka ce an ba su horo don shirin canjin kudin tsarin ba ya aiki a nan, duk inda na zagaya ban ga ko jami’i guda da ke aiki ba…,” in ji Gwamnan.