✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN ya kalubalanci cire rubutun Ajami a kan Naira

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kalubalanci karar da wani lauya ya shigar yana neman a cire rubutun Ajami a kan takardar Naira. Cif Malcolm Omirhobo,…

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kalubalanci karar da wani lauya ya shigar yana neman a cire rubutun Ajami a kan takardar Naira.

Cif Malcolm Omirhobo, ya shigar da karar gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas cewa rubutun Ajamin na alamta cewa Najeriya kasar Musulunci ce, alhali tsarin mulkin ya ce ba kasar addini ba ce.

Omirhobo wanda ya ce bai san ma’anar rubutun ba, amma yana rokon kotu ta canja shi zuwa Ingilishi ko daya daga cikin yarukan Hausa, Yarbanci ko Igbo.

A cewarsa, saka rubutun Ajami a kan Naira ya saba sashe na 10 da 55 na tsarin mulkin kasa da ya ce Najeriya ba kasar addini ba ce.

Sokiburutsu ne —CBN

Da ya ke kalubalantar karar, Lauyan CBN, Abiola Lawal, ya ce zargin ba shi da alaka da manufar CBN.

“Rubutun Ajamin kan takardun kudin ba shi da nasaba da addini ko alaka da Larabawa”, inji shi.

Babban bankin ya kuma karyata zargin cewa rubutun Ajami barazana ne ga tabbatar Najeriya a matsayin kasar da ba ta addini ba.

“Rubutun Ajamin a kan kudin Najeriya bai taba zama barazana ba ga tabbatuwarta a matsayin kasar da ba ta addini ba ko kundin tsarin mulkinta, saboda an yi rubutun ne da yardar hukumomin gwamnati da ke da alhakin hakan.

“Rubutun Ajamin da ke kan takardar Naira ya samo asali ne a shekarar 1973 bayan an canja sunan kudin Najeriya daga Fam zuwa Naira.

“Rubutun Ajamin ba tambarin Musulunci ba ne, an yi sa ne don ya taimaka wa mutune da ba su iya karatun Boko ba su iya karantawa domin bambance takardun kudi cikin sauki,” inji lauyan babban bankin.