✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

CBN ya kara tsabar kudin da za a cire zuwa N500,000

CBN ya kara tsabar kudin da kamfanoni za su iya cirewa N500,000 zuwa N5m

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara yawan tsabar kudin da ’yan Najeriya za su iya cirewa daga N100,000 zuwa Naira 500,000 a mako.

Sanarwar da babban bankin ya fitar a yammacin ranar Laraba ta kuma kara yawan tsabar kudin da kamfanoni za su iya cira a mako daga N500,000 zuwa Naira miliyan biyar.

Ta kara da cewa, “A duk lokacin da aka samu wani kwakkwaran dalilin cire fiye da hakan, za a caji kamfanoni kashi 5 cikin 100 na kudin, daidaikun mutane kuma kashi uku cikin 100.”

Sabuwar dokar takaita cire tsabar kudin dai za ta fara aiki ne daga ranar 9 ga watan Janairu, 2023.

Sanarwar, dauke da sa hannun Daraktan Lura da Harkokin Banki na CBN, Haruna Mustafa, ta ce, “Idan hakan ta faru, to dole a karbi akalla wadannan bayanan wanda zai ciri kudin, a tura a shafin CBN: Katin shaida, lambar BVN, lambar shaidar biyan haraji (TIN), da takardar sahalewar manajan banki.”

Sai dai ta ce, “Har yanzu ba za a biyan wani tsabar kudin ya haura Naira dubu 100 da wani ya ba shi ba a kan kanta.”

Wannan dai na zuwa ne baan ce-ce-kucen da aka yi ta yi kan sabuwar dokar ta CBN, wadda a kanta Majalisar Tarayya ke neman ganawa da gwamnan bankin domin a kara yawan kudin.

Majalisar ta bai wa Gwamnan Bankin, Godwin Emefiele, wa’adin ranar Alhamis, ya bayyana a gabana domin tattauna a gabanta kan dokar, tare da barazanar cewa idan bai bayyana ba, za ta soke dokar.

Sai dai sai biyu Emefiele ba ya halartar zaman, bisa hujjar ya tafi wani aiki da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tura shi kasar waje.

Sai dai kuma kasa a awa 24 da cikar wa’adin rana Alhamis da Majalisar ta ba shi, bankin ya aike mata da wasika cewa Emefiele yana duba lafiyarsa ne a kasar waje, don haka zai samu wakilci a ganawar.

Hakan ya sa ’yan Najeriya ke jiran ganin yadda za ta kaya a lokacin zaman da majalisar ta sanya ranar Alhamis.