✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

CBN ya rage kudin da bakuna ke cire wa ‘yan Najeriya

CBN ta rage N65 da ake cire wa mutum idan ya yi amfani da ATM zuwa N35.

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ba da umarnin rage kudin da bankunan kasar nan ke cire wa mutane yayin amfani da na’urar cirar kudi ta ATM da kuma tura kudin ta intanet tsakanin bankuna.

Sanarwar na kunshe ne cikin wata sanarwa da Chibuzor Efobi, shugaban sashen kula da tsare-tsaren kudi da dokoki na bankin, ya fitar a ranar Litinin, inda ya umarci bankuna da cibiyoyin kudi da su sauya tsarin cazar kudin ga ‘yan Najeriya.

CBN ya ce an dauki matakin ne saboda a tabattar bankunan na bin sabbin tsarin da kasuwanci ke tattare da shi.

Sauyin dai ya shafi N65 da ake cazar mutum idan ya ciri kudi ta ATM a bankin da ba nasa ba sau uku cikin wata daya, inda yanzu aka mayar da shi N35.

Kazalika, an sake rage cajin aika kudi ta intanet tsakanin bankuna daga N300 zuwa N50 a matsayin mafi yawan adadin da za a caji mutum.

CBN ya kuma ce ya tanadi hukuncin mai tsanani ga duk banki ko abokan huldar kasuwancin da suka ki bin sabon tsarin.