✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

N-Power: CBN zai ba wa matasa 300,000 da aka yaye rance

Zuwa karshen watan Maris ake sa ran fara biyan kudaden.

Ministar Agajiya da Ayyukan Jinkai, Sadiya Umar-Farouk, ta ce Babban Bankin Najeriya (CBN) zai ba wa matasa 300,000 da suka kammala shirin N-Power rancen domin su fara sana’o’in da suka koya.

Minista Sadiya ta bayyana haka ne a yayin jawabin da ta gabatar ranar Alhamis a wurin taron jawabin mako-mako da Fadar Shugaban Kasa ta shirya a Abuja.

Ta ce, “Muna da shirin yayen N-Power da hadin gwiwar CBN, wanda mutum 300,000 daga cikin 500,000 da suka kammala N-Power suka bayyana aniyarsu ta shiga ciki; Za a koya musu sana’o’in da suke so sannan CBN ya ba su rance su fara sana’o’in.

Ministar ta bayyaan cewa, “Mun yi nisa, har mun fara shirin bayar da horo ga masu bukata, kuma na tabbata zuwa karshen watan Maris CBN zai ba su rancen.”

A cewarta, zuwa yanzu, “Kusan mutum 109,000 da suka ci gajiyar shirin N-Power sun fara sana’o’in kansu, har suna da masu aiki a karkashin su, kuma za mu iya gabatar da shaida da ke tabbatar da hakan.”

N5,000 ta sauya rayuwar masu rauni

Ministar ta kara da cewa tunanin ’yan boko ne cewa N5,000 da ake ba wa talakawa masu ya yi kadan ya fitar da su daga kangin fatara.

Ta bayyana haka ne bayan an tambaye ta hikimar N5,000 da gwamnati ke ba wa talakawa a duk wata da nufin fitar da ’yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci.

A cewarta, ma’aikatarta ta shaida yadda N5,000 din — da wasu suka raina — da ake biyan talakawa masu rauni ke taimakawa wajen fitar da su daga matsancin talauci.

“Mutanen da ake ba wa N5,000 din tana da matukar muhimmacni a gare su, domin talakawa ne masu rauni, kuma tana kyautata musu rayuwa,” inji ta.

Ta ce duk da haka akwai ’yan Najeriya, “Irina da irinku N5,000 ba ta kai kudin katin da muke sa wa a wayoyinmu ba —bambancin ke nan.

“Amma talakawa masu rauni a karkara har suna iya ajiye wani abu daga cikin N5,000 din da ake ba su; Idan har kudin ba ya yi musu komai, ai ba tilasa su ake yi su rika yin adashin N1,000 ba. Saboda haka N5,000 tana taimakawa.

“Duk wanda ya ce N5000 ta yi kadan, to tunanin ’yan boko gare shi, domin mu ganau ne, mun je yankunan karkara, mun ga mutanen da idan aka ba su N5,000 har kuka suke yi, saboda ba su taba samun ta ba a rayuwarsu.

“Saboda haka kudin na taimakawa wajen inganta rayuwarsu daga wani mataki zuwa wani wanda ya fi shi,” inji ministar.

 

Ministar ta bayyana cewa matsalar tsaro da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas da sauran wurare ya kara kawo bukatar agaza wa mutane a Najeriya.

Unguwar yara 7,000 marasa zuwa makaranta

A jawabinsa, kodinetan shirin tallafin kyautata rayuwa, Umar Bindir, ya bayyana cewa rahoton binciken da suka gudanar a yankin Kudu ya nuna matsalar yara marasa zuwa makaranta abu ne da ya shafi kowane yanki na kasar.

Ya bayyana haka ne bayan an yi masa tambaya game ko ciyar da daliban da gwamnati ke yi ya rage yawan yara marasa zuwa makaranta.

Bindir ya ce, “Wasu idan aka yi maganar yara marasa zuwa makaranta sai su dauka almajirai da ke Arewa ake nufi, ko wani abu da ya shafi addini ko Musulunci. Amma abin da muka gano shi ne matsalar tana ko’ina a kasar nan.

“Tawagarmu da muka tura Legas sun je unguwar Mokoko, inda suka samu kananan yara 7,000 marasa zuwa makaranta da suke yawon tsintar bola. Abin ya girgiza jami’an namu.

“Irin abin da suka gani kuma ke nan da muka tura su zuwa Jos. wanda muka tura zuwa Enugu shi ma irin abin da ya gano ke nan, saboda haka matsala ce ta kasa ba wani yanki ko addini ba.”