✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN zai fara gurfanar da masu sayar da sabbin kudi

CBN ya zayyana tanadin hukuncin da za a yi wa duk wanda aka kama da laifin sayar sa sabbin kudaden.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi barazanar fara gurfanar da masu sayar da sabbin takardun kudin Naira don tsawwala al’umma.

Sanarwar da CBN ya fitar a ranar Alhamis ta ce babban bankin zai dauki matakin ne saboda dakile masu yi wa sabon tsarin zagon kasa da kuma masu likin kudi a wajen bukukuwa da taruka.

“Mun lura da yadda ake fama da dogayen layuka a injinunan ATM a duk fadin kasar nan wanda hakan ba zai rasa nasaba sa yadda wasu ke yin makarkashiya wajen karkatar da sabbin kudaden ba.

“Wani abin damuwa kuma shi ne yadda muka samu rahoton wasu mutane da ba su da rajista kuma ba ma’aikatan banki ba ke harkar musayar takardun kudi ga jama’a, a madadin CBN.

“Haramun ne a sayar da Naira, ko yin liki a wajen biki da ita.

“Don kauce wa shakku, sashe na 21 (3) na dokar Babban Bankin Najeriya na shekarar 2007 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ta tanadi cewa ‘likin kudi, kuma sayar da takardun Naira a bukukuwan aure ya saba da doka.

“Kazalika, sashe na 21(4) ya bayyana cewa ‘Haka kuma zai zama laifin da za a hukunta mutum karkashin karamin sashe na (1) idan aka kama mutum ya aikata daya daga cikin laifukan.”

Wannan dai na zuwa ne bayan da jami’an EFCC da ICPC da DSS suka fara farautar mutanen da ke sayar da sabbin kudaden duk da gargadin da CBN ya yi kan haramcin aikata hakan.