✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta fara kayyade farashin kayan kasashen waje

Babban Bankin Najeriya zai rika tantance farashin kayan da aka shigo da su daga kasashen waje

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fara daukar matakan kayyadewa da kuma lura da farashin kayan da ke shigowa Najeriya daga kasashen waje.

CBN ya ce zai rika yin hakan ne ta hanyar sabon tsarinsa na tantance farashin hajojin da yake ba wa ‘yan kasuwa masu shigo da su daga ketare canji.

“Kamar yadda ake yi a kasashen duniya, nan take CBN ya fara aiwatar da tsarin tantance farashin kayan kasashen waje domin hana tsawwala ko karya farashin kayan a cikin kasa”, kamar yadda ya sanar.

Sakon da bankin ya fitar a ranar Litinin 24 ga Agusta ya ce hakan na daga, “kokarin bankin na tabbatar da amfani da canjin da yake bayarwa ta yadda ya dace da kuma hana tsawwala farashi ko karbar ladar canji fiye da sau daya da a karshe suke komawa a kan ‘yan Najeriya masu sayen kaya.

“Ana umartar dukkannin manyan ‘yan canji da su daina bude ‘Form M’ ga masu karbar canjin ta hannun dillalai ba kai tsaye ba”, injin sanarwar ta Darektan Kasuwanci da Canjin Kudi na CBN, O. S. Nnaji.