✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN zai sauya fasalin takardar Naira

Matakin sauya fasalin takardun kudin zai kara daga darajar naira.

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayyana kudirinsa na sauya fasalin wasu takardun kudi na Naira guda uku.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa sauya fasalin zai shafi takardun kudi na naira 200 da 500 da kuma 1000.

A cewarsa, Babban Bankin wanda ya samu sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari, zai kaddamar da amfani da sabbin takardun kudin ne a ranar 15 ga watan Disamba na 2022.

Ya ce matakin sauya fasalin takardun kudin zai kara daga darajar naira.

Haka kuma, Emefiele ya sanar cewa an dakatar da cajin mutane ko sisi yayin da suka kai kudinsu asusu ajiya a bankunan kasar.