✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cedi: Yadda darajar kudin Ghana ta fadi warwas

A yayin da ake hada wannan rahoton, dala ya kai cedi 12 a Accra.

Darajar Kudin Ghana na Cedi ya fadi da kashi 3.3 cikin 100 inda canjin dalar Amurka ya kai cedi 11.3 a Accra, kamar yadda rahoton Bloomberg ya nuna. 

Rahoton ya ce, cedi ya fadi da kashi 45 cikin 100, mafi girma tsakanin kasashe 148. A yayin da ake hada wannan rahoton, dala ya kai cedi 12 a Accra.

A watan Agustan da ya gabata, gwamnatin Ghana ta kafa kwamitin gaggawa na tsarin kudi (PMC) domin ya yi nazari kuma ya kawo karshen matsalar tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

Wannan dai na zuwa ne duk da matakan da kwamitin, a karkashin jagorancin Gwamnan Bankin Ghana, Ernest Addison ya dauka domin dakile faduwar darajar Cedi sai dai ba su haifar da mai ido ba.

Gwamnatin ta kuma dora wa kwamitin alhakin kawo matakan da za su dakile faduwar darajar kudin kasar a karkashin jagorancin gwamnan Bankin Ghana.

Bayan watanni biyu, tabarbarewar tattalin arzikin kasar na ci gaba da ta’azzara yayin da kudin Cedi ya zama kudi mafi karancin daraja a duniya cikin kwanaki uku da suka wuce, kamar yadda ma’aunin darajar kudi na Bloomberg ya nuna.

Watanni biyu ke nan kasar na tattaunawa a hukumance da Asusun Lamuni na Duniya (IMF), domin samun lamuni na dala biliyan 3 cikin shekaru uku.

Muryar Amurka ta ruwaito cewa, Asusun na IMF na tafiyar hawainiya wajen amincewa saboda yana bukatar tabbatar da tsarin dorewar biyan bashin.

Dalilan da Mataimakin Shugaban Kasa, Dakta Mahamudu Bawumia ya bayar ga faduwar darajar Cedi, sun hada da magance matsalar tsarin bankuna da aka kashe kimanin dalar Amurka biliyan 7.

Sauran dalilan da Bawumia ya bayar sun hada da annobar Coronavirus da kuma yakin Rasha da Ukraine, sai dai masu fashin baki a kan harkokin kudi da tattalin arziki ba su amince da su ba.

Hamza Adam Attijjany, masani a kan tattalin arziki ya ce, bincike da Asusun Lamuni ya yi ya nuni cewa annobar coronavirus da yakin Ukraine da Rasha ba su ne dalilin faduwar darajar kudi da tattalin arzikin Ghana ba, illa iyaka dalilai na cikin gida da Bankin Ghana ya kasa magancewa.

Kamar yadda al’ummar gari ke kokawa, baya ga tsadar rayuwa, faduwar darajar kudin ya koma da sana’oinsu baya domin ko da yaushe canjin kudi na hawa ne.

A karshe Hamza Adam Attijjany ya nuna, duk matakan da gwamnati ta dauka na kara farfado da darajar cedi na kan hanya, amma gwamnati ta magance hauhawar tashin farashin kayayyaki ta hanyar bunkasa noma da inganta kayan da ake fita da su kasashen waje.

Haka kuma, gwamnatin ta shiga yarjejeniya da kasashen waje da kudin Cedi ba kudin kasar waje ba.

Sannan kuma ta san kudaden da masu zuba hannun jari ke fita da su daga kasar tare da tabbatar da cewa sun fita ne da Cedi ba kudin kasar waje ba.

A ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba kungiyar masu saye da sayarwa na Ghana (GUTA) ta fara yajin aiki a birnin Accra, domin muntsinin gwamnati ta gaggauta magance matsalar faduwar darajar Cedi.