✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cewa masu garkuwa da ni na yi sam ban san matata ba – Kwamishinan Neja

“Daga nan sai suka tambayeni ko matata ce, inda nace musu a’a."

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Neja, Alhaji Muhammad Sani Idris, ya bayyana yadda matarsa ta kubuta lokacin da za a sace shi, inda ya ce ya shaida wa masu garkuwar cewa sam ba matarsa ba ce.

Alhaji Muhammad dai ya kubuta daga hannun masu garkuwar ne ranar Alhamis bayan ya shafe kwana hud a hannunsu lokacin da suka sace shi.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da wakilin Aminiya a Minna.

A cewarsa, bayan ’yan bindigar sun kutsa kai zuwa cikin gidansa ta karfin tsiya, sai suka nufi dakin da yake tare shi da matarsa.

“Bayan sun karbe wayoyina sai suka fitoda ni waje. Hakan ya sa matata ta firgita, inda suka fara janta a kasa. Lokacin gajeren wando da singileti ne kawai a jikina.

“Daga nan sai suka tambayeni ko matata ce, inda nace musu a’a. sai suka tambayeni to me yasa muke a daki daya da ita.

“Sai nace musu daga wani bangare na gidan take, tsoron da ta ji ne yasa ta dawo inda nake.

“Cikin ikon Allah muna daidai kofar fita daga gidan ne sai wani kanena ya fito, da suka hango shi sai suka yi yunkurin harbinsa, amma ya gudu. Sai nace musu ai kanen nawa shi ne mijinta.

“Daga nan sai suka fara shawarar ko su tafi da ita ko kuma su barta, amma bayan dogon musu a tsakaninsu, sai suka yanke shawarar su rabu da ita kada ta zame musu kaya, saboda kamar ba ta cika koshin lafiya ba,” inji shi.

Kwamishinan, wanda ya fashe da kuka yayin tattaunawar ya ce masu garkuwar sun tafi da shi cikin daji inda suka yi tafiyar kimanin sa’o’i uku, kafin daga bisani su shiga wani kungurmin daji da ke kan iyakar Jihar Neja da Babban Birnin Tarayya Abuja.

“Daga nan ne suka rufe min fuska, suka daure hannuwana da kafafu na, suka bar ni ruwan sama na duka na tsawon daren ba tare da sun bani abinci ko ruwa ba, sannan suka ci gaba da azabtar da ni,” inji Kwamishinan.

Da aka tambayeshi kokwanton da mutane ke yi kan cewa ba a biya kudin fansa ba kafin a sake shi sai ya ce, “Wadanda suke kokwanto da ikon Allah dama zai wahala su yarda, amma ni da naga mutuwa kiri-kiri ina tabbatar maka da ko sisi ba a biya ba.”