✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea da United sun yi canjaras

Chelsea tana mataki na hudu a teburin Firimiyar da maki 21.

Chelsea da Manchester United sun tashi 1-1 a wasan mako na 13 a gasar Firimiyar Ingila da suka kara ranar Asabar a Stamford Bridge.

Kungiyoyin biyu sun tashi wasa ba ci a minti na 45, daga nan suka je hutu, sannan suka koma zagaye na biyu.

Saura minti uku lokaci ya cika Chelsea ta ci kwallo ta hannun Jorginho a bugun fenariti.

Cikin ‘yan wasan da suka ci kwallo 20 ko fiye da haka a Firimiyar, Jorginho ya ci fenariti 19 daga 21 da ya ci a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Daga baya ne sabon dan wasan da United ta dauka a bana daga Real Madrid, Casemiro ya farke.

Wannan shi ne wasa na 26 a Firimiyar Ingila da suka yi canjaras tsakanin Chelsea da Manchester United kenan.

Karawar da aka yi tsakanin Chelsea da United  ya nuna har a yanzu tarihi ita ce mafi yawan wasannin Firimiyar Ingila da aka tashi kunnen doki a tsakanin wasu kungiyoyin biyu.

Ciki har da karawa tara baya, bakwai daga ciki canjaras suka yi da biyar a jere.

Da wannan sakamakon Chelsea tana mataki na hudu a teburin Firimiyar da maki 21 da tazarar maki daya tsakaninta da United ta biyar.