✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta fasa sayo Ronaldo

Kungiyar kwallon kafa ta Chelasea ta janye aniyarta na daukar dan wasan Portugal, Cristiano Ronaldo.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelasea ta janye aniyarta na daukar dan wasan gaban tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo.

Da ma dai dan wasan gaban na Manchester United mai shekara 37, ya bayyana kudurinsa na barinta gabanin fara kakar wasar bana.

Ana gani wannan ra’ayin nasa na son barin Man-U ba ya rasa nasaba da rashin abun a zo a gani da kungiyar ta yi a kakar wasar da ta gabata, wanda hakan ya sa ba za ta buga wasannin zakarun turai na wannan shekarar ba.

Kocin Chelsea, Thomas Tuchel, shi ma ya jaddada cewa a yanzu kungiyar za ta mayar da hankalinta ne wajen sayen dan wasan baya.

Jawabin nasa na zuwa ne bayan kungiyar ta kammala dauko tsohon dan wasan gaban Manchester City, Raheem Sterling, dan asalin kasar Birtaniya.

Shi ma kocin Manchester United, Erik ten Hag, ya bayyana cewa ba za su sayar da Ronaldo din ba, duk da cewa dan wasan ba ya cikin tawagar masu bugawa kungiyar wasannin sada zumunta da take yi a kasar Australia.

Sai dai an danganta rashin halartar Ronaldo din da wasu uzurori da suka taso na iyalinsa.