✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta kori kocinta Frank Lampard

Ana sa ran Thomas Tuchel zai maye gurbin Lampard a Chelsea.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kori kocinta, Frank Lampard saboda rashin tabukawar da kungiyar a karkashin jagorancinsa.

Chelsea ta dauki wannan mataki na korar kocin ne duk da nasarar da kungiyar ta yi a gasar cin kofin FA a karshen mako.

Shugaban Chelsea, Roman Abramovic, ya ce “Mun shiga yanayi mara dadi, wanda dole ne mu dauki mataki, amma ina da alaka mai kyau tsakanina da Lampard.”

Chelsea na matsayi na tara a teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila, inda ta farko a gasar Manchester United ta ba ta tazarar maki 11.

Kungiyar ta yi rashin nasara a wasanni biyar daga cikin takwas da ta buga a baya-bayan nan.

Kafin fara kakar wasanni ta bana kungiyar ta kashe Yuro miliyan 250 wajen sayen sabbin ’yan wasa da suka hada da; Timo Werner, Kai Havertz, Ben Chilwell da Hakim Ziyech.

Rahotanni daga kasar Ingila na nuni da cewa tsohon kocin PSG, Thomas Tuchel ne zai maye gurbin Lampard a Chelsea din.