✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta lallasa Leicester, United za ta sallami Solskjær

Watford ta kara jefa United cikin matsala.

Kwallaye uku rigis Chelsea ta jefa a ragar kungiyar Leicester City da ta je wa bakunta a ranar Asabar.

Da wannan wasa, kungiyar ta Stamford Bridge ta hada maki 29 wanda hakan ya sa ta ci gaba da jan ragamar teburin Firimiyar Ingila bayan wasan mako na 12.

Dan wasan baya, Antonio Rudiger ne ya fara jefa wa Chelsea kwallonta ta farko a minti na 14 da fara wasan, sai Ngolo Kante ya jefa kwallo ta biyu a minti na 28, yayin da Christian Pulisic ya rufe taro da kwallo ta uku a minti na 71.

Alkaluman sun nuna cewa wannan shi ne wasa na hudu da Chelsea ta ci a waje a gasar, inda maki daya ta barar shi ne wanda ta tashi 1-1 yayin haduwar ta yi da Liverpool  mai zaman ta biyu a teburin gasar.

Chelsea ta ci gaba a gasar duk da cewar wasu fitattun ’yan wasanta na gaba na jinya da suka hada Romelu Lukaku da Timo Werner.

A ranar 28 ga watan Nuwamban Chelsea za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan mako na 13, inda ita kuwa Leicester za ta yi wa Watford masauki a ranar.

Watford ta mayar da United gidan jiya

Watford ta sake mayar da Manchester United gidan jiya bayan ta doke ta 4-1 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila da suka fafata ranar Asabar.

Wasu rahotanni na cewa, United ta yi kasa a gwiwa ne la’akari da jan kati da aka bai wa dan wasanta, Harry Maguire a minti na 69 a wasan da aka barje gumi a Vicarage.

A minti na 28 ne Watford ta jefa kwallon farko a komar United ta hannun Joshua King, inda a minti na 41 ta jefa kwallo ta biyu ta hannun Ismaila daf da za a je hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokacin United ta zare kwallo daya ta hannun Donny van de Beek, wanda wannan kwallo ita kadai ce daya tilo da kungiyar ta Old Trafford ta zira a wasan.

An kusan tashi daga wasan ne Watford ta kara kwallaye biyu ta hannun Joao Pedro Junqueria da kuma Emmanuel Dennis.

Alkalumma sun nuna cewa, wannan ne karon farko da United ta sha kashi da kwallaye da yawa a hannu sabuwar kungiyar da ta hauro gasar Firimiyar Ingila tun bayan Satumbar 1989 da Manchester Citt ta ci 5-1 a Maine Road.

A halin yanzu dai United ta yi rashin nasara a wasa hudu cikin karawa 12 a gasar Firimiyar Ingila, wanda tarihi ya nuna shin a rashin kokari karon farko tun bayan kakar 1989 da ta kammala a mataki na 13.

Mahukunta a United sun yanke shawarar korar Ole Gunnar Solskjær.

Ana tashi daga wasan da United ta sha kashi a gidan Watford ne mahukunta kungiyar kwallon kafar ta Ingilar suka shiga taron gaggawa domin tattaunawa a kan makomar kocin kungiyar, Ole Gunnar Solskjær.

Fittacen dan jarida a kan wasannin kwallon kafa, Fabrizio Romano ne ya walllafa hakan cikin wani sako a shafukansa na dandalan sada zumunta.

Ole Gunnar Solskjær

Romano ya ce galibin masu ta-cewa a Majalisar Gudanarwa ta kungiyar sun yanke shawarar a raba gari da kocin na Kasar Norway saboda rashin katabus da abun kunya da yake janyo wa kungiyar.

Sai dai Shugaban Majalisar, Joel Glazer ne zai yanke shawara kan mataki na karshe da kungiyar za ta dauka kan Solskjaer daga yanzu zuwa sa’o’i masu zuwa, inda an fi rinjayar da matakin sallamarsa kamar yadda Romano ya bayyana.