✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta lashe gasar Fifa Club World Cup

Karon farko ke nan a tarihi da Chelsea ta lashe gasar.

Chelsea ce kungiyar kwallon kafa da ta zama gwarzuwar duniya bayan ta lashe gasar cin kofin kungiyoyin kasashen duniya ta Fifa Club World Cup a daren ranar Asabar ta gabata.

Karon farko ke nan a tarihi da Chelsea ta lashe gasar bayan ta samu nasarar doke kungiyar Palmeiras ta kasar Brazil da ci 2-1.

A minti na 117 ne dai dan wasa Kai Havertz ya zura kwallon da ta bai wa Chelsea nasara, bayan kungiyarsa ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga a fafatawar da ta gudana  a birnin  Abu Dhabi da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ko a gasar cin Kofin Xakarun Turai na shekarar 2021 dan wasa Kai Havertz ne ya zura kwallon da kungiyarsa ta Chelsea ta yi nasara a kan Manchester City da ci daya mai ban haushi.

Kai Havertz rika da kofin

Wannan nasarar da Chelsea tayi ya sa ta lashe ko wacce gasa a duniya karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar, Roman Abramovich.

Tun da fari dai dan wasa Romelu Lukaku ya fara zura kwallon farko a minti na 54, kafin dan wasa Raphael Veiga ya farke ta a minti na 64, lamarin da ya kai ga an buga minti 90 da sakamakon kunnen doke.

A kan haka ne wasan ya gai ga karin minti 30, inda ana sauran minti 3 a tashi wasan kuma ya kai ga bugun fenareti, Chelsea ta samu nasarar kara kwallo daya.

Bayanai sun ce a kasar Japan aka shirya buga gasar FIFA Club World Cup ta bana, sai dai a watan da ya gabata aka sauya shawara a sakamakon karuwar adadin mutanen da cutar Coronavirus ta harba a kasar.

Ana dai gudanar da wannan gasa ce a tsakanin kungiyoyin da suka zama zakara a gasar nahiyoyi daban daban da ke fadin duniya, hadi da kungiyar da lashe gasar kasar da za ta yi wa gasar masaukin baki.