✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta lashe Uefa Super Cup

Chelsea ta lashe Uefa Super Cup a bugun fenareti.

Chelsea ta samu nasarar lashe Uefa Super Cup na bana bayan ta doke Villareal a bugun fenariti da ci 6-5.

Kungiyoyin sun tashi 1-1 a karawar da suka yi ranar Laraba, hakan ya sa suka je karin lokaci daga nan suka je bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Tun a minti na 27 Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Hakim Ziyech, sannan Villareal ta farke ta hannun Gerard Moreno a minti na 73.

Da aka je bugun fenareti ne Villareal ta barar bugunta na bakwai ta hannun Raul Albiol, wanda ya buga kwallon da mai tsaron ragar Chelsea, Kepa Arrizabalaga ya tare.

Ana dai buga Uefa Super Cup tsakanin kungiyar da ta lashe Champions League a kakar da ta wuce wato Chelsea kenan da wadda ta dauki Europa League, Villareal kenan.

Chelsea ta yi nasarar lashe Champions League, bayan da ta doke Manchester City a kakar da ta kare, ita kuwa Villareal nasara ta yi a kan Manchester United.

Karo na biyu kenan da Chelsea ta ci Uefa Super Cup, bayan wanda ta fara dauka a 1998, inda Barcelona da AC Milan ke kan gaba a yawan lashe kofin masu biyar-biyar jumulla.

Chelsea za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasan farko a kakar Firimiyar Ingila ta bana ranar Asabar 14 ga watan Agusta.