✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta sanya hannu kan yarjejeniyar dauko Timo Werner

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sanar da cimma matsaya da kuma sanya hannu a kan kwantiragin dauko dan wasan gaba na kugniyar RB Leipzig,…

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sanar da cimma matsaya da kuma sanya hannu a kan kwantiragin dauko dan wasan gaba na kugniyar RB Leipzig, Timo Werner, na tsawon shekaru biyar ranar Alhamis.

An dade ana kwan gaba kwan baya a kan yunkurin Chelsea din na dauko Werner dan shekara 24.

Zuwa yanzu, Werner ya jefa wa kungiyarsa kwallaye 32 a dukkan gasar da ya buga.

Dan wasan, wanda aka yiwa farashin Euro miliyan 60 zai ci gaba da kasancewa a kugniyar ta kasar Jamus har zuwa karshen kakar wasanni a gasar Bundesliga.

Da yake sanar da sanya hannu a kan kwantiragin a shafinsa na sada zumunta, Werner ya ce “Ina matukar farin ciki da na sanya hannu a kan wani kwantiragi da Chelsea, ina alfahari da wannan lokacin da zan koma wannan kungiya mai matukar girma”.

Dauko dan wasan dai zai kara wa Chelsea kaimi wurin ci gaba da fafatawa wurin neman gurbi a gasar Zakarun Turai a saman teburin Premier.