✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta sayi dan wasan bayan Napoli Kalidou Koulibaly

Na samu karfin gwiwar zuwa Stamford Bridge daga wurin abokaina, Edouard Mendy da Jorginho.

Chelsea ta dauki dan wasan bayan Napoli, Kalidou Koulibaly kan kwantiragin kaka hudu daga kungiyar da ke buga Serie A.

Dan kwallon mai shekara 31, dan asalin kasar Senegal, ya koma Napoli daga Genk a 2014, wadda ya yi wa wasa 317.

Zuwansa Stamford Bridge ya biyo bayan tafiyar ’yan wasan baya na Chelsea Antonio Rudiger zuwa Real Madrid da kuma Christensen da Barcelona da dauke shi, bayan karewar yarjejeniyarsu a kakar da ta wuce.

“Ina cikin farin ciki zuwa na Chelsea,” in ji Koulibaly.

“Babbar kungiya ce a duniya, kuma mafarkina a kullum shi ne na buga wasa a gasar Firimiya.

“Tun a 2016 Chelsea ta nemi ta saye ni, amma bamu daidaita ba.

“Bayan na yi magana da abokai na da suka hada da Edouard Mendy da Jorginho, sun karfafa min gwiwar da na taho nan Stamford Bridge.”

Koulibaly ya fara buga wa babbar tawagar Senegal tamaula a Satumban 2015, tun daga nan ya yi wasa 62, ya jagoranci kasar a matsayin kaftin a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2022.

Shi ne dan wasa na biyu da Chelsea ta sayo a kakar nan, bayan Raheem Sterling daga Manchester City kan fam miliyan 50, tun bayan da wasu attajirai suka mallaki kungiyar karkashin jagorancin Todd Boehly, bayan da saka wa Roman Abramovich takunkumi.

Boehly ya ce: “Koulibaly na cikin ’yan wasa masu tsaron baya da suka shahara a duniya, kwarewarsa za ta taimaka mana sosai, muna farin ciki da zuwansa Chelsea.”