✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘China ba za ta kwace kadarorin Najeriya ba saboda taurin bashi’

Hasali ma, Najeriya ta ce bashin da China ke bin ta bai wuce kaso 9.4 cikin 100 ba.

Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (DMO) ya ce ba ya cikin yarjejeniyoyin da Najeriya ta kulla da kasar China cewa za ta jinginar da wasu kadarorinta ko da ta gaza biyan bashinta.

Hasali ma, ofishin ya ce bashin da China ke bin Najeriya bai wuce Dalar Amurka biliyan 3.59 ba, wanda ke zaman kaso 9.4 cikin 100 na Dala biliyan 37.9 din da ta ciyo daga ketare.

Babbar Daraktar DMO, Misis Patience Oniha ce ta sanar da hakan yayin tattaunawarta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abuja ranar Asabar.

A cewarta, babu wata yarjejeniyar jinginar da wasu kadarorin gwamnati a cikin bashin.

A kwanan nan ne dai aka yi ta yamadidi a kafafen yada labarai da ma na sada zumunta na zamani cewa wasu kasashen Afirka, ciki har da Najeriya, na fuskantar barazanar karbe wasu muhimman kadarorinsu daga China, saboda tsabar bashin da take bin su.

Ta ce, “Ya zuwa karshen watan Satumban 2021, jimlar bashin da ake bin Najeriya shi ne biliyan 37.9, wanda ya kunshi wanda Gwamnatin Tarayya da Jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja suka ciyo daga ketare.

“Amma jimlar bashin da aka ciyo daga China bai wuce kaso 9.4 cikin 100 ba. Basussukan kuma ba sa bukatar wata jinginar kadara a matsayin sharadi, kawai yarjejeniya ce,” inji ta.

Misis Patience ta shawarci ’yan Najeriya da a kullum su rika tantance sahihancin bayanai daga hukumomi kafin su yada su.

Ta ce kafin a ciyo kowanne irin bashi daga waje, sassan gwamnati daban-daban kan bi matakai masu muhimmanci don su tabbatar da cewa bashin ya amfani kasa.