✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

China ce kasar da ta fi daure ’yan jarida a duniya —Rahoto

Kungiyar Da ke Fafutukar Kare 'Yan Jarida a Duniya (CPJ) ya gano cewa kasar China ce ta fi daure 'yan jarida

Kungiyar Kare ’Yan Jarida ta Duniya (CPJ) ta gano cewa kasar China ce ta fi daure ’yan jarida a duniya shekara ta biyu ke nan a jere.

A cewar rahoton CPJ, “China ta tsare ’yan jarida da dama da suke kokarin daukar rahoton annobar COVID-19 a shekara ta biyu ke nan a jere.

“Turkiyya ce take biye mata baya wadda ita ma ke ci gaba da kamawa da kuma gurfanar da ’yan jarida a kullum.

“Masar ce ta uku wajen yin wannan aika-aikar ba tare da gurfanar da su gaban kuliya ba, sai Saudiyya da a matsayi na hudu,” inji rahoton.

Kazalika, rahoton wanda ke fita a kowacce shekara ya gano cewa akalla ’yan jarida 274 ne aka daure zuwa ranar 1 ga Disamba, 2020, adadin da ya haura 272 da aka samu a 2016.

CPJ ta kuma gano cewa hatta a lokacin da COVID-19 ta gallabi birnin Wuhan na China, kasar ta daure ’yan jarida da dama da suke rawaito labaran da ba su yi wa gwamnati dadi ba.

Bugu da kari, CPJ ta zargi China da yi wa ’yan jaridar kasashen waje katsalandan, musamman wadanda ke aiki da kafafen watsa labaran Amurka tare da korar da dama daga cikinsu.

Ta ce kasashen da adadin ’yan jaridar da aka tsare ya karu matuka sun hada da Belarus, inda zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati ta barke da kuma kasar Itofiya.