✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

China na kokarin mamaye Duniyar Wata ita kadai – Amurka

Sai dai China ta ce zargin soki-burutsun Amurka ne kawai

Hukumar Binciken Sararin samaniya ta Amurka (NASA) ta yi zargin cewa kasar China na kokarin mamaye Duniyar Wata ta mayar da ita mallakinta ita kadai.

Shugaban hukumar, Bill Nelson ne ya yi zargin, inda ya ce kasar na kokarin mayar da wajen wani sansanin ayyukanta na soji.

Bill dai ya shaida wa wata jaridar kasar Jamus mai suna Bild cewa NASA na cikin tsananin damuwa kan take-taken na China.

“Tabbas abin damuwa ne yadda kasar China ke ci gaba da mamaye Duniyar Wata tana cewa ‘nan wajen namu na’,” inji shi.

Sai dai Zhao Lijian, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen China ya mayar da martani da kakkausar suka, inda ya bayyana zarge-zargen na Amurka a matsayin soki-burutsu.

Kasar China dai wacce ta fara zuwa Duniyar a shekara ta 2013, ta dage sosai wajen ayyuka iri-iri a wajen.

Ta kuma kaddamar da shirin harba wasu taurarin dan Adam din da za su iya zuwa Duniyar Watan, a shirye-shiryenta na zuwa Duniyar Mars nan da shekara ta 2030.

Sai dai Shugaban na NASA ya ce taken-taken na China na ayyukan soji ne, kuma tana satar fasahr wasu kasashen.

Ya ce, “Me kake tunantin China na kullawa a wadannan tashoshin nata na Duniyar? Suna koyar yadda za su lalata taurarin wasu kasashen ne kawai.

“Akwai sabuwar gasar da ake yi kan tauraron dan Adam a yanzu haka

Yakin cacar-bakin na zuwa ne a daidai lokacin da NASA ita ma ta kaddamar da wani tauraron dan Adam dinta da ta yi wa lakabi da Artemis, zuwa Duniyar Watan.

Da wannan sabon tauraron dai, ASmurka na fatan zuwa wajen Wata nan da 2024, sannan ta karasa zuwa kusa da Rana na da 2025.