✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

China za ta zafafa kamen masu damfara da kudaden ‘crypto’

Kasar ta ce zat ta sa kafar wando daya da su

Kasar China a ranar Talata ta ce za ta zafafa matakan dakile masu amfani da kudaden intanet da aka fi sani da ‘crypto’ wajen aikata damfara da zamba cikin aminci.

A cewar Hukumar sa ido kan intanet din kasar, wannan shirin ya fara ne tun farkon shekarar 2022, domin kare dukiyoyin al’ummar kasar.

Da ta ke jan hankalin manyan kafofin yanar gizon kasar kan sauke nauyin da ke kansu na gabatar da bayanai a bude, hukumar ta ce ya zuwa yanzu, gwamnatin ta rufe asusun fasahar  Weibo guda 989, da na WeChat, da kuma wani na Baidu da ya yaudari masu amfani da intanet.

Hukumar ta ce an yi amfani da shafukan wajen yaudarar mutane su zuba hannun jari a harkar crypto din da sauran kadarorin yanar gizo.

Hukumar dai ta hada hannu da kwararru inda ta rufe wasu shafukan yanar gizo 105 da ke yaudarar mutane da bayana hasashe da sauran hada-hadar crypto din.

Haka kuma, hukumar ta yi alkawarin ci gaba da dakile haramtattun ayyukan da suka shafi kudin crypton, tare da jan hankalin masu amfani da yanar gizon wajen biye wa masu hasahsen faduwa ko ribar kudin don gujewa tafka mummunar asara.