✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cibiyar CSIS ta ba wa Bulama Bukarti mukami

Ya zama babban lauya a cibiyar Tsara Dabaru, Nazari da Bincike kan Harkokin Tsaro ta Kasa da Kasa

An nada fitaccen lauyan nan mai kare hakkin dan Adam da marasa galihu, Audu Bulama Bukarti, a matsayin babban lauya a cibiyar CSIS mai Tsara Dabaru, Nazari da Bincike kan Harkokin Tsaro na Kasa da Kasa.

Bulama Bukarti ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa kan shafinsa na Twitter a ranar Talata, 1 ga watan Satumban 2020.

Audu Bulama Bukarti gogaggyen lauya ne dan asalin Jihar Yobe, amma kuma wanda ya yi karatu kuma yake zaune a Jihar Kano.

An haife shi a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1984, a garin Gashua da ke Jihar Yobe.

Matashin lauyan ya fara aikin koyarwa a Jihar Yobe bayan kammala karatun kwarewa a fannin malanta wato NCE, kafin daga bisani ya koma tsangayar koyan aikin lauya a Jami’ar Bayero da ke Kano.

Bayan kammalawa a shekarar 2011, Bukarti ya shiga aikin lauya gadan-gadan, in da yake tsaya wa marasa galihu kyauta.

Barista Audu Bulama Bukarti ya kara yin fice a lokacin zanga-zangar yaki da karin farashin man fetur da aka yi a shekarar 2011 a Najeriya, in da ya tsayawa wasu matasa da aka kama.

Audu Bulama Bukarti ya ci gaba da aikin lauya, tare da fafutukar kare hakkin jama’a, har zuwa shekarar 2014 lokacin da ya sami aikin koyarwa a tsangayar koyar da aikin lauya na jamiar ta Bayero a Kano.