Daily Trust Aminiya - Cibiyar Global Peace ta shirya bita kan zaman lafiya a Masar
Subscribe

Cibiyar Global Peace ta shirya bita kan zaman lafiya a Masarautar Kaninkon

Wata kungiya mai zaman kanta  mai suna Global Peace Foundation, da ke Kaduna ta shirya taron zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Unguwar Fari da ke Masarautar Kaninkon a Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna don tsara yadda za a gudanar da Kirsimetin bana lafiya a masarautar.

Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a Cocin ECWA 1 da ke Unguwan Fari, daya daga cikin shugabannin cibiyar, Sheikh Halliru Maraya, ya ce manufar shirya taron shi ne samar da wata kafa da za a tattauna tsakanin al’ummar yankin da suka hada da Fulani makiyaya da kabilun wurin da akasarinsu manoma ne da kuma jami’an tsaro yadda za a magance barkewar wani rikici a yankin.

Sheikh Maraya, ya ce lokaci ya yi da manoma ya kamata su rungumi ’yan uwansu makiyaya domin dukkansu iyali daya ne a karkashin Ubangiji daya.

“Musulmi da Kirista dukkansu iyali daya ne a kaa kasarkashin Ubangiji daya da suka fito daga uwa daya uba daya. Don haka ba ma son jin sake aukuwar irin abin da ya faru a bara na hare-hare a wannan yanki,” inji shi.

“Ba za mu zuba ido muna gani ana ta kashe rayuka da lalata dukiyoyi ba, don haka muka hada ku tare da jami’an tsaron da ke kula da tsaron lafiyarku don tattaunawa kan yadda za ku fahimci juna da yadda za ku rika kai kukanku wajensu da samun isassun bayanai ingantattu da za su taimaka wajen dakile duk wani abu da ka iya tayar da hankali,” inji Sheikh Maraya.

Takwararsa Rabaran Joseph Hayab, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen Jihar Kaduna, ya nanata bukatar da ke akwai ta ci gaba da gina zaman lafiya a yankin tare da samun fahimtar juna a tsakaninsu da jami’an tsaron yankin har lokacin da zaman lafiya mai dorewa zai tabbata a yankin.

“Fatarmu ita ce mu ga lokacin da zaman lafiya zai tabbata a wannan yanki,” inji shi.

A karshe ya ce babu yadda za a yi gwamnati ta iya gudanar musu da ayyukan ci gaba ba tare da samun zaman lafiya a tsakaninsu ba.

Wakilan kungiyoyin Fulani makiyaya da na manoma da ’yan sanda da Sibil Difens da sojoji da kungoyoyin mata da na matasa da shugabannin addini da na al’umma ne suka halarci taron kuma dukkansu sun tofa albarkacin bakinsu.

Idan za a iya tunawa a bara ce aka kai hari a yankin da ke masarautar Kaninkon a jajibarin Kirsimeti wanda ya jawo zaman tankiya a tsakanin kabilun yankin da Fulani makiyaya.

More Stories