✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cikar Jigawa Shekaru 30: Badaru Ya Taka Rawar Gani

Wani jan aiki na gina jiha tun daga tushe, wacce ta ke daga yanayi na faƙo da duwarwatsu, zuwa garuruwa da suka zama maraya, da…

Wani jan aiki na gina jiha tun daga tushe, wacce ta ke daga yanayi na faƙo da duwarwatsu, zuwa garuruwa da suka zama maraya, da ake ganin kamar ba zai yiwu ba, sai ga shi ta ya tabbata.

A halin yanzu, Jihar Jigawa ta hau kan wani kadami na cigaba, wanda ya samu ne sakamakon hobbasar da gwamnoninta suka yi, musamman Sule Lamido da Badaru Abubakar.

Kirkirar Jihar Jigawa a ranar 27 ga watan Agusta, 1991, da Shugaban Kasa a wancan lokaci, Ibrahim Badamasi Babangida ya yi, ya kuma sanya babban birnin jihar ya kasance a Dutse ya girgiza al’ummar jihar da ma kasa baki daya.

Sannan matakin ya haifar da bacin rai ga al’ummar jihar.

Idan ka tattara irin ayyukan da gwamnonin baya suka yi, tun daga kan Kanar Olayinka Sule, Ali Sa’ad Birninkudu, Birgediya-Janar Ibrahim Aliyu, Kanar Rasheed Shekoni da Laftanar-Kanar Abubakar Zakari Maimalari zuwa Ibrahim Saminu Turaki, Jigawa ba ta isa ta bigi kirji ta ce ta samu cigaba ba.

Sule Lamido ya gaji jiha wacce take ta noma ce amma kuma ta samu koma baya wajen tattalin arziki, ilimi, sannan kan al’ummarta a rarrabe yake.

Kai, a kowanne matsayi na ci gaba, an bar Jigawa a baya.

A zangonshi na farko a matsayin gwamna, Lamido ya fi mai da hankali a kan bunkasa ilimi, inda ya gina sama da ajujuwa 1,000 a fadin jihar kuma dukkansu da bencinan zama.

Ya kuma samar da kananan makarantun sakandare 21 gami da makarantun makiyaya har 216 a fadin jihar, har ma ya samar da jami’a.

Haka nan kuma Lamido ya samar da bunkasar gine-gine da dama da ma sauran abubuwan more rayuwa domin ya dora jihar a kan gwadabe na ci gaba.

A lokacin da aka rantsar da Muhammad Abubakar Badaru a matsayin Gwamnan Jihar Jigawa a shekara ta 2015, ya gabatar da wani jawabi mai cike da hikima, inda ya bai wa al’mmar jihar tabbacin cewa zai kai su ga tudun-mun-tsira.

A watan Afrilu na 2015, Badaru ya ce, “Tushen mulkin da za mu aiwatar zai ba da karfi ne a kan tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, samar da ingantacciyar rayuwa ga jama’a, ruwan sha, ingantaccen kiwon lafiya, sama wa matasa aikin yi, sama wa mata sana’o’i da kuma yaki da talauci ta hanyar inganta aikin noma da kiwo”.

Bisa wannan jawabi da Badaru ya yi, ya kasance daya daga cikin gwamnoni kalilan a Nijeriya da suka yi fice wajen dora jihohinsu bisa tafarkin cigaban zamani na karni na 21.

Irin manyan ayyuka da Gwamna Badaru yake kan gudanarwa a jihar sa sun burge Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, lokacin da aka gayyace shi kaddamar da wasu daga cikin su saboda yawansu da kuma ingancin su a ranar 1 ga watan Yuli.

A cikin shekaru shida kawai,  gwamnan ya biya bukatun al’ummar jihar, inda ya sama musu ci gaban da har suna ganin daidai suke da sauran sa’annin jihohi da ke Arewaci da ma Yammacin kasar nan.

Nazarin da duk mai karatun wannan rubutu zai yi na shekaru shida da Badaru ya yi a matsayin gwamna zai sa ya fahimci cewa ba karamin aiki ya yi ba wurin sama wa Jihar Jigawa cigaba.

Tun daga harkar ilimi, samar da lafiya, hanyoyi, aikin noma, sashen ma’aikatar gwamnati da sauran sassa, Gwamna Badaru ya samu manyan nasarorin da samun sama da su abu ne da kamar wuya.

Abu na farko da ya aiwatar bayan ya hau karagar mulki shine inganta hanyoyin samar da kudaden shiga na jihar, wadanda da su ya yi amfani wurin aiwatar da manyan ayyukan da ya yi a jihar.

A lokacin da ya hau mulki, Badaru ya tarar da kudin shigar jihar N2,343,974,525.10 ne a shekara ta 2015, amma zuwa shekara ta 2019 kudin ya karu zuwa N8,537,371,114.59.

A sashen ma’aikatan jihar, Gwamna Badaru ya yi gyara da nufin tsarkake sashen ta hanyar bankado ma’aikatan bogi 4,888 da ake biya albashi, a dalilin hakan gwamnati na samu rarar N90,194,000 a kowane wata.

A lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hau mulki, ya zo da alkawura guda uku da suka hada da yaki da rashawa, samar da tsaro da kuma fadada hanyoyin tattalin arziki.

Bangaren bunkasa tattalin arziki da Buhari ya fi bai wa muhimmanci shine noma, wanda shi ma Badaru ya bai wa muhimmanci ke nan.

Tun da fari ma, Badaru a tsarin gwamnatinsa, ya yi amfani ne da samar da sauyi da cigaba wurin zakulo irin kwarewar da jihar ke da ita a fannin noma.

Wannan sai ya kasance abin da ya rika bunkasa karfin cinikayya a jihar.

Wannan tsari nasa ya yi daidai da irin wanda Gwamnatin Tarayya ke kokarin aiwatarwa don ganin an rage dogaro da man fetur a kasar.

Ta hanyar anfani da cewar “Noma Sana’a ce”, a kan hakane gwamna ya zaburar da jama’ar jihar, musamman matasa zuwa ga sana’ar noma, wato, na duke tsohon ciniki, wanda a wannan lokacin yake tattare da matsaloli da dama da ba su dace da ci gaban zamani ba.

Wannan rashin ci gaban ya samar da koma-baya da karancin abin da ake girba, wanda ya bar manoman a cikin tsananin talauci, duk da cewa jihar tana da damammaki da suka hada da filin noma hekta miliyan 1.8 da kuma hekta 400,000 na noman fadama da za a iya anfani da shi a rani da damuna, sannan kuma ga wadatattun madatsun ruwa da za a iya sama wa matasa aikin yi.

Gwamnatin Badaru ta fara da fitar da ingantaccen tsarin noma na zamani ta yadda zai bunkasa tattalin arzikin jihar ta hanyar samun yawaitar kayayyakin noma da kuma girbi.

Gwamnatin ta samu wannan nasara ne ta hanyar tsare-tsaren ci gaban noma na DFID da suka hada da SPARC, PERL, ENABLE2 da kuma GEMS3 da ke gudana a jihar.

A lokacin da ya karbi mulki a 2015, Badaru ya lura da cewa bangaren ilimi na daf da rushewa.

Sashen na tattare da matsaloli da suka hada da rashin gine-gine, karancin diban dalibai, rashin kwararrun malamai, rashin kayan aiki, da kuma rashin damar karo ilmi ga ’yan jihar.

Sauran matsalolin sun hada da rashin ingantattun gidajen malamai, yawaitar yara marasa zuwa makaranta, rashin litattafai, da kuma rashin ingantaccen tsarin ilimi da kulawa da kuma kudaden gudanarwa.

Ganin wadannan tarin matsaloli, gwamantin ta Badaru ba ta yi kasa a gwiwa ba inda ta jawo masu ruwa da tsaki a fadin jihar domin ganin an warware matsalolin.

Wannan ne ya kai ga samar da wani sabon tsari mai taken canjin manufa ga tsarin ilimi a jihar, wato (Education Change Agenda), wanda wannan ya dora bangaren a kan wani gwadabe na daki-daki wanda kuma zai dauki lokaci mai tsawo kafin a cimma nasara.

“A ziyarar da na kai wa wasu makarantu a jihar, na ga dalibai na karatu a cikin mumunar yanayi.

“Ba za mu yarda da wannan lamarin ba. Na dauki alkawarin samar da kyakyawan yanayin karatu ga yaranmu” inji Badaru a watan Augusta na shekara 2015.

A karkashin wannan tsarin na sauya wa sashen ilimi manufa an gina ajujuwa 6,679 tare da gyara wasu.

An kuma dauki kwararrun malaman makaranta 5,973 aiki, an samar da kujerun makaranta 185,086 da ma gadajen kwanciya masu sama da kasa na daliban dake ma karantun kwana.

Haka kuma Gwaman ya tallafa wa makarantun Islamiyya guda 516 da ke kananan hukumomi 27 da ke jihar.

Ya kuma samar da gidajen kwanan malamai guda 254, ofisoshi 6, dakunan kwanan daliban kananan sakandare 8, makewayu 4,746 a makarantun da ke jihar.

Duba da irin wannan gagarumin aiki, Badaru ya kafa babban tarihi da zai yi wuya a samu wanda zai wuce shi a jihar.

Ba bukatar sai an yi ta yada cewa Badaru ya yi ayyuka, wadanda ya gada da wadanda ya samar, domin kuwa ya sauya akalar jihar inda ya mayar da ita jiha babba mai tsayuwa a cikin tsara kamar yadda aka ambata a cikin wannan rubutu.

An kashe biliyoyin Naira wurin ganin an inganta rayuwar al’ummar jihar ta hanyar gina tituna, gadoji, samar da ruwan sha da sauran su.

Haka kuma, wani muhimmin sashe da Badaru ya inganta shi ne gina rayuwar matasa. Ba wanda zai karyata irin kaunar da matasa a jihar ke nuna masa saboda yadda ya inganta musu rayuwa tun daga hawansa mulki a shekara ta 2015.

Kididdiga ta nuna cewa matasa 152,593 ne suka amfana daga tsare-tsaren tallafi a karkashin gwamnatin Badaru daga 2015 zuwa 2020.

Haka kuma bincike ya nuna cewa ta hanyar anfani da tsarin koyar da sana’a, Badaru ya magance zaman banza a tsakankanin matasa a Jihar Jigawa wadda ta kasance a cikin jihohi na gaba-gaba wurin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Sarari da kuma lokaci ba za su isa a iya kididdige irin ayyukan da Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya aiwatar ba a cikin shekaru shida na kasancewarsa gwamnan jiha.

Duk da haka, kamar yadda masu magana ke cewa, “Ayyukan ake gani ba surutun ba”, gwamnan ya kawo sauyi na ci gaba a Jihar Jigawa da ya yi daidai da karni na 21, ta yadda a ke lissafa jihar a matsayin daya daga cikin kananan jihohin da suka samu ci gaba a Najeriya.

Wadannan nasarori da aka samu sun nuna cewa shugabanci na gari shi ne mafita wajen samar da ayyukan alheri ga jama’a. Allah Ya kara ba wa jiharmu shugabanni nagari.

Daga Jaafaru M. Kaugama, Dutse, Jihar Jigawa.
[email protected]