✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cin kashin shanu na tsaftace jiki da ruhi – Likita

Cin kashin shanu yana kara zurfin tunani da karfafa ruhin dan Adam.

Wani kwararren likitan yara mai suna Dokta Manoj Mittal daga Jihar Haryana a kasar Indiya, ya jawo ce-ceku-ce a shafukan Intanet, bayan da ya fito a wani bidiyo yana yabon fa’idar cin kashin shanu, a lokacin da yake cikin ci.

Masana magungunan gargajiya na Indiya sun dade suna amfani da kashin shanu a matsayin magani ga duk wani marar lafiya da ya kamu da cuta kamar ta kansa da Coronavirus, amma wannan amincewar ba ta hada da kwararrun likitoci wadanda suka yi imani da abubuwa na kimiyya da gwajin asibiti ba.

Manoj Mittal, Manaja Darakta daga Karnal, Gundumar Haryana, ya fito a cikin wani bidiyo da aka wallafa kwanan nan inda tun daga lokacin ya fara yaduwa, yana cin wani bangaren kashin shanun yana yaba fa’idar cin sa a jiki, wajen kara zurfin tunani da karfafa ruhin dan Adam.

“Kowane bangare na (Panchagabya) wato kashin shanun da masu bautar gargajiya ke amfani da shi, don neman tabarruki yana da matukar amfani ga dan Adam,” inji Mittal.

Ya ce, “Duba, idan muka ci kashin saniya, to jikinmu da tunaninmu sun zama tsarkakku. Ranmu ya zama tsarkakke. Da zarar ya shiga jikinmu, yana tsarkake jikinmu.”

Likitan ya kara da cewa, mahaifiyarsa ta kasance tana buda baki ta hanyar cin kashin saniya kuma matan da suke shan kashin saniya ba sa bukatar a yi masu tiyata a lokacin haihuwa.

A cikin bidiyon, ana iya ganin Dokta Manoj Mittal yana dibar dunkulellan kashin saniya yana ta ci a hankali kamar burodi.

Sai dai yana samun martani daban-daban a shafukan sada zumunta. Yayin da wadansu jama’a da suka yaba masa kan rungumar maganin gargajiya na Indiya, wadansu kuma suna zarginsa da yin watsi da ilimin kimiyya don ya yada wannan hauka.

“Ya kamata Majalisar Likitoci ta Indiya ta lura da wannan kuma ta soke lasisinsa na aikin likita. A matsayinsa na likitan yara, bai kamata ya rubuta irin wannan ikirarin ga kananan yara marasa laifi ba,” kamar yadda wani mai amfani da Facebook ya wallafa.

“Shaidar digirin likitanci ko digirin kashin shanu,” kamar yadda wani ya yi sharhi.