✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cin zali kawai wasu cibiyoyin tsaro ke yi —Monguno

Mashawarcin Shugaban Kasa ya ba da umarnin rushe haramtattun cibiyoyin tsaro

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Babagana Monguno ya ba da umarnin rushe duk hukumomin tsaro da aka kafa ba bisa ka’ida ba a Najeriya.

Monguno, ya bayyana haramtattun hukumomin tsaron a matsayin barauniyar hanyar cin zali da amshe kudaden jama’a.

Ya gargadi mutane da hukumomin cikin gida da na waje kan ayyukan cibiyar NATFORCE, mai ikirarin sanya ido kan shigo da kananan makamai Najeriya.

Hadimin Shugaban Kasar ya ce Cibiyar Kula da Kanana da Matsakaitan Makamai ta Kasa, karkashin Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, ce kadai ke da ikon yin wannan aikin.

Gidan Talabijin na Kasa (NTA) ya ruwaito shi a ranar Lahadi yana gargadin NATFORCE cewa kada ta kuskura ta yi katsalandan a hurumin da ba nata ba.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro da su taimaka wajen kawar da haramtattun cibiyoin tsaron, domin Najeriya na shirin aiwatar da yarjejiyar kungiyar ECOWAS kan dakile yaduwar kanana da matsakaitan makamai.

Najeriya da wasu kasashen Afirka na kungiyar ECOWAS, musamman a yankin Sahel na fama ’yan ta’adda da masu tsattsauran ra’ayin addini da ake danganta ayyukansu da yaduwar makamai barkatai.

Ana ganin aiwatar da sashe na 24 na yarjejeniyar ECOWAS kan kawar da kanana da matsakaitan makamai zai taka muhimmiyar rawa wajen dakushe kaifin matsalolin tsaro a yankin.

Najeriya da kashen Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso da Mali da sauransu na fama da matsalar da ta’addancin kungiyar Boko Haram da ISWAP da dangoginsu da suka dauki makamai.

An shafe kimanin shekara 12 ana gwabza fada da kungiyoyin ’yan tawayen, duk da rundunar hadin gwiwa da kasashen suka kafa domin tunkarar matsalar.

Dubban mutane sun mutu, wasu sun yi gudun hijira, baya ga asarar dukiya mai tarin yawa da aka yi a sakamakon ayyukan kungiyoyin a yankin.