Cin zarafin da ’yan Afirka ta Kudu ke yi ga ‘yan Najeriya | Aminiya

Cin zarafin da ’yan Afirka ta Kudu ke yi ga ‘yan Najeriya

    i-mail: aminiyatrust@yahoo.com; Tes: 08075129644

Salam Edita. Da fatar kana lafiya. Don Allah ka ba ni dama domin in nuna bacin raina game da muzgunawa da cin zarafin da mutanen kasar Afirka ta Kudu ke yi ga ’yan Najeriya mazauna kasarsu. Ko shakka babu wannan muzgunawar an dade ana yi wa ’yan Najeriya a kasar, domin ko a bara cin zarafin da aka yi wa ’yan Najeriya a kasar ya yi matukar muni.

Sai dai duk da wannan danyen aiki da ake yi wa ’yan Najeriya a Afirka ta Kudu, ina shawartar ’yan uwana matasan Najeriya su sani cewa, hakan ba shi ne zai ba mu damar auka wa kayayyakinsu ko na ’yan uwansu da ke Najeriya ba. Domin an ce idan rai ya bace to hankali kada ya gushe, kasancewar yin hakan tamkar kara wa su ’yan Najeriya mazauna kasar bakin jini ne. Maimakon haka shugabanni ya kamata su bi abin ta fuskar diplomasiyya, idan za su iya kai kasar Afirka ta Kudu Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya.

Don haka muna shawartar gwamnatin Najeriya ta yi duk mai yiwuwa wajen nemo wa ’yan ƙasarta hakkokansu a kan wadannan azzalumai.

Daga Ashiru Lawal Nagoma Ruwan-Ɓaure (Ɗan Kishin Talaka) Jihar Zamfara. 08139177665

Rashin amincewa da rufe iyakoki abin takaici ne

Assalamu alaikum Edita. Hakika rashin amincewa da wadansu al’ummar Najeriya suke yi a kan rufe iyakokin kasashen makwabtan kasata Najeriya abin takaici ne lura da yadda wannan lamari zai sa talaka musamman manoman kasar dariya da kuma walwala.

Da fata hukumomin da alhakin haka ya shafa za su kara kaimi wajen rufe duk wata hanya wadda za ta kawo baraka don kawo wa manoma nakasu a harkar nomansu a kasata Najeriya.

Daga karshe nake kiran al’ummar Najeriya mu ba da hadin kai wajen kawo ci gaba mai ma’ana a daukacin kasar nan da kuma addu’ar fatar alheri ga shugabanni.

Daga Abbas Baffah Cheledi Jihar Bauchi. 08120304020.

Tambaya ga Buhari kan rufe iyakokin Najeriya

Shugaba Buhari mun ji ka kara garkame iyakokin kasarmu, wai don hana shigowa da makamai da shigo da shinkafa da sauran kayan masarufi. Tambayata ga Buhari shin wayar salularsa da akwatin talabijin dinsa da agogonsa da tsala-tsalan motocin da yake hawa da sauran wasu kayayyakin da yake  amfani da su duk a Najeriya ne aka yi su? Da fata Buhari ko mukarrabansa za su ba ni amsa.

Daga Haruna Muhammad Katsina, Shugaban Kungiyar Muryar Jama’a, 07039205659.

Fatar alheri ga Buhari a taron Majalisar Dinkin Duniya

Assalam Aminiya. Mu al’ummar Najeriya fatarmu tafiyar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi zuwa kasar Amurka don halartar taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya karo na 74 da ke gudana Allah Ya sa a fara lafiya a gama lafiya Ya dawo da shi gida lafiya.

Daga Usaina Alhaji Umar Foreber Gashuwa  08108003333.

Asibitin Doko na bukatar tallafin gaggawa

Assalamu alaikum Edita. Don Allah ku isar mana da sakon kokenmu zuwa ga mai girma dan Majalisar Tarayyarmu mai wakiltar Garki da Babura, Alhaji Adamu Mohammad Fagen Gawo ya kawo wa asibitunmu tallafin gaggawa. Yana fama da matsalolin da suka yi masa tarnaki da dabaibayi musamman a bangaren haihuwa. Akwai karancin kayan aiki da rashin wadatattun gadajen kwantar da marasa lafiya wanda a sakamakon wadannan matsalolin asibitin yake kokarin durkushewa. Da fatar kiranmu ya isa ga kunnuwan da aka yi dominsu.

Daga Mutawakkil Gambo Doko, Karamar hukumar Garki, jihar Jigawa, 07032695589

Bincikar Katin Zama Dan Kasa a Arewa maso Gabas

Fatan alheri ga dukkan ma’aikatan AMINIYA. Ku ba ni dama in tofa albarkacin bakina, kan sanarwar da jami’an tsaro suka fitar inda suka ce za su fara bincikar Katin Shaidar Zama Dan Kasa  (National ID Card) a yankin Arewa maso Gabas, domin zakulo  batagarin da suka rage a cikin al’umma. Alal hakika muna maraba da wannan mataki matukar za a yi binciken bisa tsari da mutunta juna tsakanin matafiya da jami’an tsaro. Domin a baya an yi irin wannan bincike amma wallahi ba mu ji dadinsa ba, domin ana amfani da wannan dama ce wajen cin zarafin mutane musamman baki wadanda suke fitowa daga sauran sassan kasar nan. Saboda haka muna kira da babbar murya ga jami’an tsaronmu su gudanar da wannan binciken bisa tsari. Ya Allah Ka taimaki jami’an tsaron Najeriya Ka ba su nasara a kan ayyukansu a kasar nan, amin summa amin.

Daga Idriss M. Idriss, Damaturu JIhar Yobe 08033775767.

A hana mai watsa wa yara kudi a Damaturu

Muna masu kai kokenmu ga Gwamnatin Jihar Yobe da ta tarayyar Najeriya su taimaka mana mu al’ummar Karamar Hukumar Nguru. Yara kanana suna samun raunuka duk mako, sanadiyyar wani bawan Allah da ke zuwa duk mako yana watsa kudi a kan kwalta.

Yara ba sa zuwa wuraren ayyukansu na yau da kullum duk karshen mako, sai dai ka gansu a kan kwalta ko’ina suna jira a zo a watsa musu kudi, wanda dalilin haka akwai wadanda yanzu haka suke kwance a asibiti saboda raunuka da suka samu.

Muna kira ga mahukunta su taka wa wannan mutum birki, domin kauce wa abin da zai kai ya kawo nan gaba.

Daga Kwamared Salisu Armaya’u Nguru. Dan Kungiyar Muryar Talaka. Reshen Jihar Yobe, 08069383959.

Mun yaba da dakatar da sabuwar dokar bankin CBN

Hakika matakin dakatar da sabuwar dokar da Babban Bankin Najeriya ya dora kan ajiyar kudi a bankuna da Majalisar Dokokin Najeriya ta yi abu ne mai kyau. Domin matakin babban bankin zai jefa ’yan Najeriya cikin halin ka-ka-ni-ka-yi.

Daga Abdulmalik Sa’idu Mai Biredi, Tashar Bagu Gusau, 08069807496.

Kira ga Gwamnatin Kano

Salam Edita. Don Allah a mika mini kirana ga Karamar Hukumar Kunchi da gwamnatin Kano kan su yi wa Allah su kalli al’ummar Matan-Fada a karamar hukumar a taimaka a gyara musu hanyarsu daga Kunchi zuwa Matan-Fada zuwa Roni.

Daga Lawan Yaro Baba Bichi ’Yandadi 09023326156.

Maraba da Gadar Ibi

Assalam Editan Aminiya da fatar kowa yana cikin koshin lafiya amin. A gaskiya na yi matukar farin cikin da na karanta labarin gadar Ibin nan. Allah Ya tabbatar da alheri, amin.

Daga Saminu Artillery Yelwa Shendam Jihar Filato 08032436477, 08027091994.

Ina kaunar Ganduje saboda kaunar jama’ar Kano

Salam. Don Allah Edita, ka ba ni dama in bayyana wa duniya yadda nake kaunar Gwamnan Kano Dokta Ganduje kamar yadda nake kaunar ’yan uwana na jini. Saboda tunda nake a duniya ban taba ganin Gwamnan da ya tallafi rayuwar talakawan Kano sama da Ganduje ba. Wannan kaunar da yake yi wa jama’ar Kano da yadda ya inganta fannoni da dama na rayuwar mutanen Kano ta sa na ji ina kaunarsa har zuciyata kamar yadda nake kaunar ’yan uwana. Fatata Allah Ya hada ni da shi wata rana domin in bayyana masa irin kaunar da nake yi masa.

Daga Shehu Mansur S. Getso 0814609692.

A biya tsofaffin ma’aikatan

Kano hakkinsu

Assalam Editan Aminiya. Don Allah ka ba ni fili don in yi kira ga gwannatin Kano kan don Allah ta ji tausayin tsofaffin ma’aikata ta biya su hakkinsu na barin aiki (garatuti). Ma’aikata fa ba kamar ’yan siyasa suke ba, wadanda suke dibar kudi yadda suka ga dama, ma’aikata almajirai ne a tausaya musu.

Daga Husaini Tsoho Imawa  Kura 08165610365.

Fatan alheri ga Gwamnan Zamfara

Assalamu alaikum Edita. Ku ba ni dama in gai da Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Mutawalen Maradun. Allah Ya kara maka lafiya da nisan kwana da sauran mukarrabanka baki daya.

Daga Muhammadu Musa Mai Haki Sabuwar Kasuwa, Gusau 07067887164.

Tura dalibai Kasar waje: Jinjina ga Kwankwaso

Salam Editan, ina son ka taimake ni da wannan fili namu na jinjinawa Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, game da tura dalibai kasashen waje kuma ‘ya’yan talakawa da fatan Allah ya sa ka zama shugaban kasar Najeriya amin, gaba dai gaba dai Kwankwaso.

Daga Alhaji Jinjiri na Alhaji Shuaibu Mile 12, Legas 09023489162.

Gargadi ga Yarbawa

Assalam Edita da fata kana nan lafiya. Ina son in yi amfani da wannan damar in gargadi Yarbawa a kan tsanar da suke wa Hausawammu da suke zaune a yankinsu. Abu kadan zai faru za ka ga ana ta ci wa Hausawammu mutunci a can. Misali abin da ya faru a Legas da aka samu sabani tsakanin Hausawa da Yarbawa, da aka kira ma’aikata da zuwansu sai suka goyi bayan Yarbawan. Ina son su sani cewa, akwai Yarbawa da dama Arewa wadanda muke zaune da su ba ma takura musu. Muddin za su rika takura wa namu mu ma za mu iya ramawa a kan nasu.

Daga Nasir Kano 09069985179. 

Ta’aziyyar Bashir  Musa Liman

Allah Ya jikan Bashir Liman da rahma Ya kyautata makwancinsa Ya sa halinsa nagari  ya bi shi. Ya sada shi da Annabin Rahma (SAW). Ya Allah Ka ba wa iyalansa hakurin rashinsa Ka sa Aljannar Firdausi ta kasance masaukin dukkan Musulmi, amin.

Daga Faeeza Edreth Ya’uee Gombe 09030041241.

Rashin zaben kananan hukumomi a Katsina

AMINIYA ’yar amana ku gaya wa  Gwamnatin Jihar Katsina rashin gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar ba karamin zagon kasa ba ne ga gwamnatin Buhari. A ce yau akalla shekara hudu da rabi babu zaben kananan hukumomi a jihar mu ta Katsina, Kananan hukumomin sun zama kufai tamkar an kammala yaki a tekun fasha. Daga 08155648155.

A sakarwa Kananan hukumomi kudaden su

Assalamu alaikum, kira ga Gwmnonin Nageriya akan maganar kudaden Kananan hukumumi talakawa su ne mafi kusa da Karamar hukuma an wayi gari al’umma suna fama da talauci Gwamnonin Najeriya har dai talakawa suke mulki to su sakarwa Kananan hukumomi kudadensu Allah Ya basu ikon sakar musu hakkokinsu.

Daga Tijjani Ibrahim Kano Karamar Hukumar Fagge. 09030235649.

Fatan alheri ga jaridar AMINIYA

Assamu alaikum, ina yi ma jaridar AMINIYA fatan alheri.

Daga Ma’ajin Kungiyar Zabi Sonka ta jihar Zamfara Shu’aibu Maji Dadi Mairoba Birnin Tudu Gummi 08136070219.

Kira ga hukumar daukar malaman Kano

Assalam, kira ga hukumar daukar malaman firamare ta jihar Kano, ku ji tsoron Allah wajen daukar ’ya’yan marasa gata talakawa, marasa kowa a sama sai Allah.

Daga Tukur  Maraya Shanono, 07032442923.

Kira ga Gwamnan Jihar Sakkwato

Assalamu alaikum Edita, da fatan kana lafiya ina kira ga Aminu Waziri Tambuwal da ya ji tsoron ALLAH akan tsaron jahar Sakkwato. Domin ana kashe mutane ba gaira ba dalili saboda haka muna fata Gwamna zai maida hankali, bayan haka ina fatan gwamna zai cika alkawari hanyar gada zuwa Dukamaje Allah Ya sa muda ce ameen.

Daga Bashar Garbati Dukamaje 08167791483.

A lura da adadin jami’an tsaro

Don haka bangarori suke ta hankoron ko ta yaya sai sun dare kan mulki. To wannan ya taimakawa tabar barewar tsaro a kasa. Ya kamata ace an maida hankali wajan lura da adadin jami’an tsaron da ya kamata ace muna dasu a kasar nan. Nawa jan hankalin Allah Ya bada iko.

Daga Abubakar Plumber Loko Goma Abuja, 07039508352.

Jinjina ga Dan Majalisa mai wakiltar Kiru

Assalam Edita, dan Allah a mikamin sakon gaisuwata zuwa ga Dan Majalisa mai wakiltar Kiru Honorabul Kabiru Hassan a bisa ayyukan da yake yi na alheri Allah Ya saka mai da alheri amee, Allah Ya sa sauran ’yan majalisar su yi koyi da shi amin.Daga Dan Adawa Mai A.C Kogo Kofar Kudu 09030466517.