✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cin zarafin mace: Kotu ta yanke wa Sanata Elisha Abbo hukunci

Wata Babbar Kotun Abuja da ke zamanta a Apo, ta umarci Sanata Elisha Abbo da ya biya naira miliyan 50 a matsayin tarar cin zarafin…

Wata Babbar Kotun Abuja da ke zamanta a Apo, ta umarci Sanata Elisha Abbo da ya biya naira miliyan 50 a matsayin tarar cin zarafin wata mata da ya yi a wani shagon sayar da kayan wasanni na jima’i.

Lauyan da ke kare hakkin karar mai lamba FHC/CV/2393/19, Lugard Tare-Otu, ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter yana cewa Kotun ta umarci Sanata Abbo ya biya matar hakkin tozarcin da ya yi wa matar.

A ranar 11 ga watan Mayun 2019 ne wata na’urar daukan hoton bidiyo ta nado Sanatan mai wakiltar shiyyar Adamawa ta Arewa a Majalisar Dattawa, yana ta marin matar, Osimibira Warmarte a shagon.

Cikin wani rahoto da sashen Hausa na BBC ya ruwaito, wasu bayanai sun ambato Sanatan cike da nadama yana neman gafara tare da neman a yafe masa da cewa ba halinsa bane tozarta mata.