✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Cin zarafin mata na karuwa a kafofin sadarwa na zamani a Najeriya’

Babban Daraktan Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma (CITAD) Y. Z. Ya’u ya ce ana samun karuwar cin zarafin mata ta kafofin sadarwa…

Babban Daraktan Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma (CITAD) Y. Z. Ya’u ya ce ana samun karuwar cin zarafin mata ta kafofin sadarwa na zamani a Najeriya.

Daraktan ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da cibiyar ta shirya a Kano, inda ya ce akwai bukatar samar da hanyoyin kawo karshen cin zarafin matan ta kafofin sadarwar, domin hakan na shafar ci gaban Najeriya

A cewar sa, sun gano hakan ne sakamakon bayanan da suke tattarawa tsawon shekara biyar.

Ya kuma ce faifan bidiyon da aka yada na daliban makarantar Chrisland da ke Legas, da kuma a baya-bayan nan yadda wasu suka sace wata mata da daya daga cikinsu ya hadu da ita a kafar Sada zumunta a matsayin mummunan cin zarafin yanar gizo.

Haka zalika ya ce wadannan abubuwa sun sanya iyaye da mazaje na dakatar da ’ya’yansu mata da matayensu daga amfani da kafofin, wanda kuma hakan nakasu ne ga rayuwarsu, inji shi.

Ya kara da cewa ko a yanzu jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta koma kan intanet, don haka ne cibiyar ta tashi tsaye ta shirya taron domin jan hankalin al’umma kan hatsarin hakan.

Haka kuma ya ce wannan matsala ba ta takaita ga masu karancin shekaru ba, har da ma’aikata da yan siyasar cikinsu, musamman a shafukan sada zumunta, wanda hakan ya sanya suke da karanci a sahar.

“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dauki wannan batu da muhimmanci, tare da ba wa kwamitin da ta kafa domin lalubo mafita ga kare kananan yara a shafin intanet, da ya bullo da wannan tsari ga mata” inji shi.

Shugaban cibiyar ya kuma ce akwai bukatar gwamnatin ta samar da daidaito tsakanin jimsin maza da mata wajen amfani da yanar gizon, domin hakan zai taimaka matuka wajen magance fargaba da cin zalin da ake wa matan.