✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cin zarafin ’yar jarida: Abin da doka ta tanada kan daukar hoton jami’an tsaro a bakin aiki —Lauyoyi

’Yan sanda sun lallasa wata ’yar jarida a Kano bayan ta dauki hotunansu suna tsaka da aiki.

Wasu lauyoyi a Najeriya sun ce babu inda Doka ta hana al’umma daukar hoto ko bidiyon jami’an tsaro da waya ko kyamara lokacin da suke gudanar da aiki.

Lauyoyin biyu – Barista Abba Hikima da Amina Umar Hussain – sun yi wannan fashin baki ne a shirin Inda Ranka na Freedom Radio a Jihar Kano.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake zargin wasu ’yan sanda sun lallasa wata ’yar jarida, Naziha Ibrahim ma’aikaciyar Rahama Radio da ke Kano, bayan ta dauki hotunansu suna tsaka da aiki.

’Yar jaridar dai ta sha duka har sai da aka kai ta asibiti, sai dai rahotanni na nuna shalkwatar rundunar ’yan sandan ta gayyace ta bayan ta samu sauki, domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Barista Amina ta ce daukar jami’an tsaro a waya ko kyamara ba laifi ba ne ko kadan a Dokar Kasa, hasalima za a iya amfani da shi a kotu a matsayin shaida.

“Babu wata doka da ta fito karara ta ce kar ka dauki bidiyonsa, ko hotonsa yana aiki, ni dai a bincikena ban gani ba.

“Kuma idan ka duba akwai shari‘ar da Kotun Koli ta yi a shekarar 2020, wanda ta yi maganar cewa idan dan kasa ya yi niyyar ko yunkurin gabatar da electronic evidence (shaidar da na ’ura ta nada) wanda waya tana ciki, za ka iya gabatar da wannan abubuwan a matsayin shaida.

“Dokar ta kuma zayyana jerin sharudda da matakan da za ka bi wajen gabatarwar.

Shi ma wani fitaccen lauya Barista Abba Hikima ya ce Sashe na 22 na Kundin Dokar Najeriya, ya bai wa al ’umma damar daukar hoto ko bidiyon dan sanda lokacin da yake gudanar da aikinsa.

“Dokokin Najeriya sun ba wa ‘yan Najeriya damar su dauki ma‘aikatan tsaro hoto yayin da suke aiki. Kuma za su iya daukarsu da waya, ko kyamara ba laifi.

“Kuma idan muka duba inda aka ci gaba, da Najeriyar ma ana amfani da kyamarar CCTV inda ake daukar kowa da kowa akan titi. To me ya sa ba a hana wannan ba?”, in ji Hikima.

Barista ya ce hasslima dokar Najeriya ta karfafi mutane su dauki hoto ko bidiyon  ’yan sanda lokacin da suke bakin aiki, domin taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu, da kuma idan sun yi ba daidai ba a samu hujja akansu, kamar yadda su ma suke neman hujja akan mutane masu laifi.

“Mene ne kake tsoro don a dauke ka a hoto in dai ba daidai kake yi ba? Saboda haka duk wanda ke babatu ko kokarin cewa ba a kyauta ba an dauke shi a hoto, ko ya nemi cin zarafin mutum, to za mu kaddara ba daidai yake yi ba,” in ji shi.