✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Cinikayya tsakanin Najeriya da China ta kai ta $12b a 2021’

Jakadan kasar China a Najeriya Cui Jianchun ya ce, cinikayya tsakanin kasashen biyu ta karu da kashi 7.1  wanda hakan ya sa jimlarsa ta kai…

Jakadan kasar China a Najeriya Cui Jianchun ya ce, cinikayya tsakanin kasashen biyu ta karu da kashi 7.1  wanda hakan ya sa jimlarsa ta kai Dala biliyan 12 a shekarar 2021.

Cui ya fadi haka ne a wani taron bikin makon al’adun gargajiya na kasashen biyu, cikin jerin shagulgulan bikin murnar zagayowar ranar ‘yancin kan Najeriya 62, da kuma dangantakar kasashen biyu.

Jakadan na China ya ce, Najeriya ita ce babbar abokiyar cinikin kasarsa a nahiyar Africa, don haka Najeriya sai ta dage, ta samar da kayyakkin da ita za ta rika kaiwa Chaina at sayar.

Mista Chui ya yi farin ciki da karfafuwar danganta tsakanin kasashen biyu, sannan ya yi alfahari da manyan ayyuka da kasarsa ta sa hannu ake kuma gudanar da su.

Aikin cike teku na Lekki a jihar Legas don samar da tashar jirgin ruwa, da aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta Zungeru, da kuma matatar Mai ta Dangote da za a kaddamar da su a shekarar 2023.

A na sa jawabin, Shugaban Hukumar Kula da Inganta Al’adun Gargjiya ta Kasa, Otunba Olusegun Runsawe ya gode wa Ofishin jakadancin na Chaina da samar da yanayi da kuma damarmaki da za su kara inganta alaka tsakaninsu.

Ranar daya ga watan Oktoba, wacce Najeriya ke bikin samun ‘yancin kai kuma ya zo daidai da cika shekaru 72 na cika jamhuriya a China, a wannan shekara kuma  kasashen biyu ke cika shekara 51 da kulla kawancen kasa da kaka.