✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ciwon kafa ya addabi mutumin da ya yi tattakin nasarar zaben Buhari

Mutumin da ya taka daga Gombe zuwa Abuja saboda Buhari na neman kudin magani

Mutumin da ya yi tattaki domin murnar zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Jam’iyyarsa ta APC a 2015 na neman taimako saboda ciwon kafar da ya hana shi sakat.

Dahiru Buba, wanda dattijo ne dan asalin Karamar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe, na daya daga cikin mutanen da suka yi tattaki zuwa Abuja tun daga garinsu.

A yanzu dai Dahiru na fama da ciwon kafa mai tsanani, wanda ya kai shi da mika kokon bararsa zuwa ga uwar jam’iyyar APC akan ta taimaka masa da abin da zai yi amfani da shi wurin jinyar kafar tasa.

Dahiru ya kwashe kimanin kwanaki 15 yana taka sayyadarsa yayin tattakin zuwa birnin Abuja a wancan lokacin.

Hakan dai ya sa har sai da shugabancin APC ya yaba da kaunarsa ga nasarar jam’iyyar tare da ba shi shaidar yabo da jinjina.

Malam Dahiru ya ce, “Tun daga lokacin dana gudanar da tattakin kafata ta hana ni sakat, hakika zan ji dadi idan jam’iyyar ta taimaka min na warke”.