✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ciwon sanyin da ke hana mutane cin nama

Ciwon sanyi mai kama gabobin dan adam, wanda a turance ake kira da Rheumatoid Arthritis yana daya daga cikin cututtukan da ke hana wanda ya…

Ciwon sanyi mai kama gabobin dan adam, wanda a turance ake kira da Rheumatoid Arthritis yana daya daga cikin cututtukan da ke hana wanda ya kamu da shi cin wasu nau’ukan abinci ciki har da nama.

Wannan ciwo yana dauke da alamomin kumburi, kaikayi da zafi a mahadar gabobin jiki,  kuma yana lahani musamman a gabobin guiwar kafa da hannu.

Me ke sa a kamu da cutar?

Likitoci sun bayyana cewa wannan cutar takan bi jinin mutum a matsayin gado kuma ana iya kamuwa da ita daga baya ko da iyayen mutum ba su da cutar.

Bincike ya nuna cewa yawan kiba da nauyin jiki yana jawo wannan ciwo, haka kuma bayyana jiki a wuraren sanyi yana jawo sanyi ya zauna a gwiwowin mutum.

Magani
Akwai hanyoyi kala-kala da za’a iya bi wajen samun kariya ga wannan ciwo. A cikin su akwai:

Motsa jiki: Bincike ya  nuna cewa yawan motsa jiki yana kawo sauki wa masu wannan jinya kuma yana kara karfafa aikin kasusuwan da cutar da shafa.

Canjin abinci: Masanan ilmin magunguna sun bayyana cewa sanya ganyayyaki, wake, man zaitun, a cikin tsarin abincin mutum  yakan kawo sauki da kuma taimaka wa ga karin lafiyar jiki.

Har ila yau yawaita cin naman shanu yana kara zafin wannan ciwo,  saboda haka, ya kamataa hana duk wanda ke dauke da wannan cutar cin naman shanu, sai dai ana iya cin naman kifi da kaji.

Tiyata da magungunan asibiti: Yana daga cikin abubuwan da za’a iya yi ma mai dauke da ciwon gaba.

A karshe, mai wannan cuta ya kula da  shan suga da cin kayan filawa; a dai na shan taba da giya, a kuma yawaita cin soyayyen abinci.