✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CONUA haramtacciyar kungiya ce —Lauyan ASUU

ASUU ta lashi takobin maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan yi wa CONUA da NAMDA rajista

Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya (ASUU) ta lashi takobin maka Gwamnatin Tarayya a kotu ka yi wa kishiyarta, sabuwar kungiyar Malaman jami’a ta CONUA rajista.

ASUU ta lashi takobin garzayawa kotu ne bayan Gwamnatin Tarayya ta ba da lasisi ga Gamayyar Kungiyoyin Malaman Jami’a (CONUA) da kuma Kungiyar Malaman Fannin Likitance da Gabtu na Jami’o’i (NAMDA).

Lauyan ASUU, Femi Falana (SAN), ya ce, kafa CONUA da NAMDA ya haramta, don haka, “ASUU za ta je kotu, kuma Kotun Ma’aikata za ta je”.

Falana ya bayyana haka a hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels, inda yake kalubalantar rajistar da ka yi wa kungiyoyin biyu.

A makon jiya ne Ministan Kwadago Chris Ngige ya bayar da lasisi ga kungiyoyin CONUA da NAMDA a Abuja, yana mai cewa za su yi aiki tare da ASUU.

Ana zargin kafa CONUA da NAMDA wani yunkuri ne daga Gwamnatin Tarayya na karya lagon ASUU, wadda ta shafe wata takwas tana yajin aiki.

A tsawon lokacin, ana ta Kai ruwa rana tsakanin bangarorin biyu, ba tare da samun daidaito ba.

ASUU tana yajin aikin ne domin matsa wa Gwamnatin Tarayya ta cika alkawuran da ta yi wa jami’o’i na a inganta su da wadata su da kayan aiki tun a shekarar 2009.

Kungiyar na kuma neman gwamnatin ta biya malamam jami’a hakkokinsu da suke bin ta bashi.

Sauran bukatun sun hada da neman gwamnatin ta cire su daga tsarin biyan albashi na IPPIS — wanda suke zargi da rashin inganci da kuma tauye musu hakkoki — da dai sauransu.