✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Copa Del Rey: Barcelona ta tsallaka matakin kusa da na karshe

Barcelona ta zagaya matakin kusa da na karshe na gasar Copa Del Rey.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta samu tikitin zuwa matakin kusa da na karshe a gasar Copa Del Rey bayan doke Real Sociedad da ci daya mai ban haushi.

Dan wasan gaban Barcelona, Ousmane Dembele ne ya zura kwallo daya tilo a raga a minti ma 54.

Real Sociedad ta samu koma baya a wasan, bayan da alkalin wasa ya bai wa dan wasan tsakiyarta, Braiz Mendez jan kati a minti na 40 da fara wasan.

Hakan ya sanya kungiyar ta daina kai hare-hare tare da tarewa a gida don tare farmakin da Barcelona ke kai mata.

Sai dai ba jimawa da dawowa daga hutun rabin lokaci, Dembele ya saka Barcelona a gaba.

Akalla mutum dubu 85 ne suka shiga filin wasa na Camp Nou don kallon wasan.

Barcelona na ci gaba da jan zarenta a bana, bayan ta lashe kofin Super Cup a hannun Real Madrid, wadda ta doke da ci 3 da 1 a Saudiyya.

Kazalika Barcelona na ci gaba da jan ragamar teburin Gasar Laliga ta Sifaniya da maki 44 daga wasa 19, yayin da Real Madrid ke biye mata a baya da maki 41 daga wasa 19.