✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Adamawa na shirin rufe iyakokinta

Daga karfe 12 na daren ranar Talata gwamnatin Adamawa za ta rufe dukkan hanyoyin shiga ko fita daga jihar har tsawon mako biyu, a wani…

Daga karfe 12 na daren ranar Talata gwamnatin Adamawa za ta rufe dukkan hanyoyin shiga ko fita daga jihar har tsawon mako biyu, a wani yunkuri na hana cutar Coronavisrus yaduwa.

Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ne ya fadi hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Fintiri ya ce yanke wannan shawara ya zame masa dole domin jihar na iyaka da kasar Kamaru.

Ya kar da cewa za a dakatar da zirga-zirgar babura da motocin haya a cikin jihar a tsawon wadannan kwanaki 14.

Ya kuma bayyana cewa da gwamnati ta bayar da umarni cewa ma’aikata su zauna a gida, hakan ya ci tura, shi ya sa ya rufe iyakokin jihar ganin yadda cutar ke ci gaba da yaduwa a Najeriya.

Fintiri ya ce an hana duk wani taron biki da ‘yan zaman majalisa da guraren sayar da barasa amma an bai wa shagunan sayar da maguna da da na abinci da gidajen mai da kuma bankuna  su ci gaba da harkokinsu.

Tuni dai jihohin Najeriya da dama suka dauki irin wannan mataki don ganin sun hana annobar Coronavirus yaduwa zuwa yakunansu.

Sai dai kuma wasu masana na ganin daukar wannan mataki bai isa ba, tun da cutar kan dauki lokaci kafin a gano mutum na dauke da ita, don haka akwai bukatar a yawaita wuraren yin gwaji don tabbatar da ba a yi kitsi da kwarkwata ba.