✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An gargadi mutane kan kiyaye dokar zama a gida

Shugaban karamar Hukumar Sanga da ke jihar Kaduna, Charles Danladi ya bukaci jama’ar karamar hukumar da su ci gaba da hakuri tare da kiyaye dokar…

Shugaban karamar Hukumar Sanga da ke jihar Kaduna, Charles Danladi ya bukaci jama’ar karamar hukumar da su ci gaba da hakuri tare da kiyaye dokar zama a gida da gwamnatin jihar Kaduna ta sanya har zuwa lokacin da za a samu saukin yaduwar cutar coronavirus.

Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin zama da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro da aka gudanar a hedkwatar karamar hukumar da ke Gwantu ranar Alhamis, inda ya gargadi masu karya doka da su guji haduwarsu da fushin hukuma a duk lokacin da suka shiga hannu.

Mista Danladi ya kuma shawarci masu ibada daga dukkanin addinai da su guji tarukan jama’a kowane iri a wuraren ibada, maimakon haka su zauna tare da yin bauta da addu’o’insu a cikin gidajensu har zuwa lokacin da lamari zai sauya wanda kuma gwamnati ce ke da alhakin sanar da hakan.

Hakazalika ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su guji bude wuraren kasuwancin su da sauran wurare.

Taron ya samu halartar hukumomin jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji da jami’an tsaro na farin kaya da suka hada da: Sibil Difens da jami’an tsaron farin kaya na DSS da ‘Yan Banga da kuma shugabannin addini.