✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus: An kwaso ‘yan Najeriya 102 daga Masar

‘Yan Najeriya 102 sun dawo gida daga kasar Masar bayan hana sufurin jiragen sama da ya yi sanadiyyar makalewar wasu ‘yan Najeriya a wasu kasashe.…

‘Yan Najeriya 102 sun dawo gida daga kasar Masar bayan hana sufurin jiragen sama da ya yi sanadiyyar makalewar wasu ‘yan Najeriya a wasu kasashe.

Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama ya sanar da dawowan ‘yan Najeriyan ta shafinsa na Twitter a daren Juma’a.

Onyeama ya kara da cewar karin wasu mutum 260 za su dawo kasar daga kasar Indiya da safiyar yau Asabar.

Tun da farko Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya da ke Kasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa ta ce ‘yan Najeriya da za a kwaso daga Indiya na da dab da fara hawa jirgin da zai dawo da su zuwa Abuja.

Abike ta kara da cewata ce dukkansu an yi musu gwajin cutar COVID-19 kuma babu wanda aka samu yana dauke da kwayar cutar.