✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An sallami ragowar masu cutar a Kebbi

An sallami mutum biyu da suka rage masu dauke da cutar coronavirus a jihar Kebbi bayan sun warke daga annobar. Ragowar mutum biyun an sallame…

An sallami mutum biyu da suka rage masu dauke da cutar coronavirus a jihar Kebbi bayan sun warke daga annobar.

Ragowar mutum biyun an sallame su ne a yau Alhamis bayan sakamakon gwajin da aka yi musu ya nuna sun warke.

Kwamishinan Lafiyan jihar Kebbi, Jafar Muhammad ya sanar da haka a sashen killace masu coronavirus a Cibiyar Lafiya ta Jihar da ke Kalgo.

“Za su koma su ci gaba da mu’amala a cikin al’umma domin gwaje-gwajen da aka kara yi sun tabbatar da warkewarsu,” inji shi.

Kwamishinan ya kara da cewa yanzu ke nan babu sauran mai dauke da cutar ta COVID-19 a fadin jihar.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Taraba ta sallami mutun na karshe mai cutar bayan ya warke.