✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An shirya bude wuraren ibada da na shakatawa a Legas

Gwamnatin Legas ta shirya bude masallatai da coci-coci dama wuraren shakatawa a jihar. Shugaban ma’akatar kare lafiya ta jihar Mr Lanre Shitu ne ya shaida…

Gwamnatin Legas ta shirya bude masallatai da coci-coci dama wuraren shakatawa a jihar.
Shugaban ma’akatar kare lafiya ta jihar Mr Lanre Shitu ne ya shaida haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai akan aniyar gwamnatin Legas na bude harkokin tattalin arzikin jihar .
Yace ma’aikatar kare lafiyar al’ummar jihar ta shirya tsaf domin fara rijistar wuraren da za a bude, kana tuni ma’aikatar ta fara tuntubar masu ruwa da tsaki a sha’anin tare da hadin gwiwar ma’aikatar cikin gida, da yawon bude ido da al’adu.
Ya kara da cewa tuni gwamnatin jihar ta fidda manhajar bude wuraren da abin ya shafa.