✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus ba za ta hana aikin Hajji bana ba —Saudiyya

Tabbas duk musulmi idan ya ji wannan zai yi farin ciki.

Mahukuntan Kasar Saudiya sun bayar da sanarwar cewa, a bana maniyata daga sassan duniya za su samu damar sauke farali, sabanin shekaru biyu da cutar Coronavirus ta tilasta dage aikin Hajjin.

Ma’aikatar Kula da Ayyukan Hajji da Umara ta Saudiyya ce ta sanar da hakan a ranar Lahadi, inda ta ce a kwanan nan za ta fitar da adadin maniyatan da za a bai wa kowacce kasa damar sauke farali a bana.

Hukumar Alhazzai da kuma masu kamfanonin shirya aikin Hajji da Umara a Najeriya, sun yi marhabin da wannan sanarwa da mahukuntan Saudiyya suka fitar.

Musulmai da kuma Hukumar Alhazai ta Najeriya sun bayyana jin dadinsu game da matakin dage haramcin saukar jiragen Najeriya a Saudiyya da kuma sanarwar yiwuwar aikin Hajjin na bana.

“Tabbas duk musulmi idan ya ji wannan zai yi farin ciki kan dage wannan doka da aka yi, a cewar Ustaz Abubakar Muhammad Saddiq.

“Allah ne Kadai Ya san dan wannan shekaru biyu da ba a yi aikin Hajjin ba mutum nawa wanda Hajjin nan ya wajaba a kansu, sun samu kudi har sun mutu ba su samu damar sauke wannan farali da ke kansu ba.

“Yadda aka samu wani abu da ya gusar da wannan tsaiko na rashin gudanar da aikin hajjin dole zai yi wa musulmi dadi, kuma nasara ce ga addini da taimako a gare shi. ”

Hukumar Alhazan Najeriya ta ce wannna mataki zai bai wa maniyatan da suka ajiye kudadensu shekara da shekaru damar sauke farali a bana.

Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa, Kwamishinan Jigilar Alhazai na Kasa, ya ce “mutane wanda tun shekarar 2019 ba su je aikin Hajji ba, haka 2020 da 2021, kudadensu na wurin Hukumomin Alhazai na Jihohi.

“Kuma muna jaddada cewa, wadanda suka fara zuwa suka bayar da kudaden ajiyarsu, a basu fifiko lokacin da aka zo shirye-shiryen aikin Hajji, kuma hakan zai sa su gamsu cewa an musu adalci.

Nafisatu Abdullahi, wata daga cikin wadanda suka bayar da ajiyar kudadensu tun shekarar 2020, ta ce “mun ji dadi da jin wannan labari, Allah Ya sa bana da mu za a yi, don shekara biyu ke nan yanzu muna jira.”