✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Dalilin dage taron gasar wakoki

Mawakin siyasar nan da ke zaune a birnin Kano, Nazifi Sharif, ya dage taron raba kyaututtuka ga wadanda suka yi nasara a gasar da ya…

Mawakin siyasar nan da ke zaune a birnin Kano, Nazifi Sharif, ya dage taron raba kyaututtuka ga wadanda suka yi nasara a gasar da ya shirya a kan wakarsa ta ’Hanta da Jini‘.

Mawakin ya dauki wannan mataki ne, a cewarsa, saboda halin da ake ciki na bullar cutar Coronavirus, har sai al’amura sun daidai ta.

Tun da farko dai mawakin ya shirya zai gudanar da taron raba kyaututtuka da suka hada da mota da keke Napap da babur da kudade ga wadanda suka zamo zakaru a gasar ne ranar Lahadin a Kaduna.

“Da farko an shirya cewa za a rufe wannan gasar ce a ranar 30 ga watan da ya gabata, sannan alkalan gasar su duba wadanda suka yi nasara, tun daga na daya har ya zuwa na goma, kuma a ba su kyaututtuka a wannan taro da aka daga.

“An shirya cewa wannan taro zai sami halartar gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i da Sanata Uba Sani da shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawal da sauran manyan baki daga jihohi”.

A cewar mawakin idan an sami saukin wannan annoba za a sake sa ranar taron.

“Tun da an daga wannan taro za mu sake bude kofa ga wadanda ba su sami damar shiga wannan gasa ba, domin su sami damar shiga. Ya zuwa yanzu dai, mutanen da suka shiga wannan gasa, maza da mata, sun kai 830”.