✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Gwamnati ba ta da wani tsari —Balarabe Musa

Gwamnatin Najeriya ba ta da tsarin da za ta iya magance matsalar coronavirus, inji tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa. Tsohon gwamnan…

Gwamnatin Najeriya ba ta da tsarin da za ta iya magance matsalar coronavirus, inji tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa.

Tsohon gwamnan ya fadi hakan ne lokacin da yake bayyana yadda yake kallon jawabin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da maraicen Litinin.

A cewar Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, akwai matsaloli manya kusan guda hudu a kasar nan tun kafin zuwan coronavirus wadanda kuma gwamnatin ta kasa magance su, don haka yake ganin ba za ta iya da wannan ba ma.

COVID-19: Dole ce ta sa mu tsawaita dokar hana fita —Buhari

Coronavirus: Majinyatan Kano ba su da alaka da juna

“Coronavirus daya ce kawai daga cikin matsalolin [Najeriya]; kuma coronavirus din nan barnar da take yi na rai da dukiya bai kai ta wasu ba.

“Misali dubi rashin tsaro—asarar da ake yi saboda rashin tsaron nan ya rubanya asarar ma da ake yi a coronavirus.

“…[A]sarar da ake yi ta mutane saboda yunwa da rashin kiwon lafiya ta fi wadanda ke mutuwa saboda coronavirus.

“Kuma ga sace-sacen mutane da ake yi da na dukiyar jama’a…‎.

“Gaskiya saboda Allah gwamnatin Najeriya ba ta da tsarin da za ta magance matsalar coronavirus domin ta gaza maganin bala’o’i hudu kafin coronavirus din”.

Tallafi ga talakawa

Da ya juya ga alkawarin da Shugaba Buhari ya yi na tallafa wa marasa galihu kuwa, tsohon dan siyasar cewa ya yi me jiya ta yi ballantana yau?

“Misali, maganar taimaka wa gajiyayyu da abinci sun kasa, domin taimakon da muke ji da ake bai wa mutane bai kai wanda zai wuce na rana daya ba.

“Ba ma zaton gwamnatin Najeriya na da tsari da karfin magance wannan matsala, domin manyan kasashen duniya da suka ci gaba kamar su Amurka da Birtaniya ma ba za su iya magance wannan abu ba, sai dai su da yake sun ci gaba suna kokarinsu…

“Wadanda kurum za su iya magance wannan abu su ne kasashe ’yan gurguzu inda shi ke duk dukiyar kasa ta jama’a ce kuma ana amfani da ita ta haka”, inji Alhaji Balarabe Musa.

Ko jawabin zai yi tasiri?

Duba da wadannan abubuwa da ya fada, shin a ganin tsohon gwamnan, jawabin na da wani tasiri kuwa?

“Eh, yana da tasiri domin gwamma a yi amfani da shi da a ki yin amfani da shi.

“Domin [idan aka ki yin amfani da shi] bala’in sai ya fi haka; komai gazawar gwamnati—duk da mun san wannan gwamnatin ta gaza—amma komai gazawarta abin da za ta yi ya fi abin da kai za ka yi ko ka yanke hukunci da kanka”.

Tsohon gwamnan na tsohuwar jihar Kaduna ya kuma bayyana rashin jin dadinsa da yadda Shugaba Buhari ya takaita jawabin nasa a kan Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun kawai, saboda a ganinshi, kamata ya yi “idan shugaban kasa zai yi magana ya yi magana a kan abin da yake shafar kasa gaba daya.

“Kuma ya fitar da hanyar da jihohi za su bi wajen magance matsalar.

“Yanzu misalin karin zama a gida da ya ce a yi ai magana ya yi kurum a kan Legas da Ogun da Abuja amma kuma ai abin Najeriya ya shafa baki daya”.

‘Abubuwan da jawabin ya rasa’

Abu na biyu da Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ke ganin ya kamata shugaban kasar ya yi magana a kai amma bai yi ba shi ne, “jawabi a kan yadda ake sace wasu daga cikin abubuwan da aka ce a raba wa jama’a domin hana yin hakan, amma bai yi ba”.

Sai dai kuma duk da hakan, inji tsohon gwamnan, akwai abin dubawa a tsawaita dokar hana fita a wuraren da aka ayyana.

“Gaskiya dole a goyi bayan gwamnati a kan wannan sha’ani domin babu zabi kuma akwai hatsari idan ba a goyi bayan gwamnati ba.

“Ita kuma gwamnati za ta dogara ne da malamai da suka san tarihi kuma suna [da karfin] fada a ji.

“Kuma tilas a saurari masana da likitoci da sauran [ma’aikatan lafiya].

“Kuma abin da gwamnatin Najeriya ke yi dangane da wannan matsala gwamnatocin duniya ma haka suke yi; duk kasashen duniya da suka ci gaba da wadanda ma ba su ci gaba ba duk abin da suke yi ke nan domin su kare bala’in da ke aukuwa yanzu”, inji Alhaji Balarabe Musa.

Da maraicen Litinin ne dai Shugaba Buhari ya gabatar da jawabin, wanda a ciki ya ce ya zama dole a tsawaita dokar hana fita a jihohin Legas da Ogun da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya.

A cikin jawabin, Shugaba Buhari ya ce a makwanni biyu na dokar, an yi nasarar gano fiye da kashi 90 cikin 100 na mutanen da ake bibiya saboda sun yi mu’amala da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar.

’Yan Najeriya da dama sun bayyana ra’ayinsu a kan wannan jawabi da kuma sakwannin da ya kunsa game da yakin da ake yi da annobar coronavirus a Najeriya—yayin da wasu ke suka, wasu na sambarka.