✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Gwamnatin Kano ta yi feshin magani

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta yi feshin maganin kashe kwayoyin cuta a wuraren taruwar jama’a da wuraren ibada. Wata sanarwa mai dauke da sa-hannun…

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta yi feshin maganin kashe kwayoyin cuta a wuraren taruwar jama’a da wuraren ibada.

Wata sanarwa mai dauke da sa-hannun kakakin Ma’aikatar Kula da Muhalli Abbas Habeeb ta ambato Kwamishinan Muhalli na jihar, Dokta Kabiru Getso, yana cewa feshin wani bangare ne na matakan da ake dauka don hana annobar COVID-19 yaduwa.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Dokta Getso yana cewa an yi feshin ne a kasuwanni da masallatai da majami’u da sauran muhimman wuraren taruwar jama’a a cikin kwaryar birnin Kano da kewaye da kuma sauran manyan garuruwan jihar.

“Wannan feshi daya ne daga cikin matakan kan-da-garki da gwamnati ke dauka don hana yaduwar annobar. Gwamnati na yaki da annobar ta ko wacce fuska.

“Don haka tsaftace muhalli wani muhimmin lamari ne a wannan lokaci, kuma feshin maganin kashe kwayoyin cuta abu ne mai matukar muhimmanci wajen tsaftace wuraren taruwar jama’a masu yawa irin su masallatai da majami’u da kasuwanni”, inji kwamishinan.

Tuni dai gwamnatin ta Kano ta rufe iyakokin jihar ga masu shiga ko fita in ban da ababen hawan da ke dauke da kayan abinci ko magunguna ko sauran abubuwa masu matukar muhimmanci.