✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus: Karin mutum 12 sun warke a Legas

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da karin mutum 12 da suka warke daga cutar coronavirus a jihar. Sanwo-olu ya sanar da hakan ne…

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da karin mutum 12 da suka warke daga cutar coronavirus a jihar.

Sanwo-olu ya sanar da hakan ne a shafinsa na twitter inda ya shaida cewa tara cikin mutanen da suka warke aka kuma sallama maza ne, uku mata da kuma ‘yar kasar Ukrain a cikin su.

Ya kara da cewa, zuwa yanzu mutum 199 suka warke daga annobar Coronavirus a jihar Legas.

Zuwa yanzu Jihar Legas ita ke kan gaba da yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da Coronavirus a Najeriya.