✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Kwamiti ya ki raba kayan tallafin da aka ba shi

Wata biyu da bayarwa a raba wa jama'a, kwamitin bai raba ba.

Majalisar Dokokin Jihar Neja ta gano mota casa’in da daya na tallafin kayan abincin cutar coronavirus da aka ki rabawa, watanni biyu bayan hannanta su ga kwamitin yaki da cutar a jihar.

Kwamitin Majalisar kan cutar ya yi takaicin rashin raba kayan rage wa jama’a tasirin bullar cutar, wanda masu taimakawa suka bayar gudunmuwa ga gwamnatin jihar domin saukaka wa jama’a halin rayuwa.

Da yake caccakar kwamitin yaki a cutar, Shugaban Kwamitin Majalisar Abdulmalik Madaki Bosso ya ce, “Ta yaya za a jibge kayan abinci sama da wata biyu, a ce ana jiran wadanda sauka bayar su fitar da tsarin yadda za raba”?

Ya fadi haka ne bayan shugaban kwamitin jihar Ibrahim Ahmed Matane ya ce suna jiran bayanin tsarin rabon kayan ne daga wadanda suka bayar da su, sannan kwamitinsa ya raba wani sashe na kayan a lokacin dokar kulle.

Amma Kwamitin Majalisar ya ce duk da cewa gwamnatin jihar ya Neja ta sassauta dokar kulla, jama’a suna shan wahala da yunwa saboda tasirin cutar, don haka babu hujjar taskance abincin.

“Saboda haka ku yi abin da ya kamata domin karbar tsarin da suke so a abi na raba kayan nan ba da jimawa ba”, a cewarsa.

An bankado kayan ne a lokacin zagayen sa ido da Kwamitin Majalisar ke yi a cibiyoyin killace masu cutar da rumbunan adana abincin jihar.

Kayan sun hada da mota 88 na kayan abinci daga Gamayyar Kamfanoni na Yaki da COVID-91 (CACOVID-19) da kuma mota uku daga Gwamnatin Tarayya.

Abubuwan da ke cikin dakunan ajiyar sun hada dubban buhunan shinkafa da sukari da garin tuwo, sai kuma dubban kwalaye na taliya a taliyar zamani.